“Ilimin ’ya mace ya fi muhummanci akan na namiji”
Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Hajiya Naja`atu Malam Bala Rabi`u ta fito ne daga gidan malanta domin kuwa ta fito ne daga zuri`ar Sheik Muhammadu Rabi`u mahaifi ga marigayi Khalifa Sheik Ishaƙa Rabi`u Khadumul ƙur`an wacce kuma ta yi karatun zamani tun daga makarantar rainon yara har zuwa digiri da digirgir a Bayero.
Kafin ita maza ne ke samun wannan damar zuwa jami`a a wannan zuri`a, kuma ta bayyana muhimmancin ilimin mata, irin ƙalubalen dake cikin neman karatun da kuma nasarori da ta samu a rayuwarta da yadda ya kamata mace mai karatu ta kasance mai biyayya ga mijinta.
Sannan kuma ta bayyana mana yawan `ya`yanta, da kuma yadda take faɗakar da ɗalibai, sai kuma yadda take tafiyar da hidimar aure da aikin koyarwa a lokaci guda harma da abinda tafi kauna ko sha`awa a rayuwa.
Wakilinmu Muhammadu Mujittaba bin Usman ya samu tattaunawa da Dakta Naja`atu wacce wakiliyar shigar kuɗi da fitarsu ce a Jami`ar KHAIRUN dake Kano wato Bursar a Khalifa Isyaka Rabi`u University Kano.
MANHAJA: Da farko masu tare damu na buƙatar jin tarihinki a taƙaice.
NAJA’ATU: Sunana Naja`atu Malam Bala Rabi`u, ɗan uwa ne shaƙiƙi ga Sheik Ishaƙ Rabi`u khadimul ƙur`an, dukkaninsu rahamar ubangiji ta lululuɓesu.
Matsayina kuma shi ne, ni ce Bursar wato babbar wakiliyar kuɗi a jamai`ar KHAIRUN wato Khalifa Isyaka Rabi`u. A ɓangaren tarihi a taƙaice, an haife ni a birnin Kano kuma kamar yadda na faɗa a baya Alhaji Rabi`u shi ne mahaifina, mahaifiyata Hajiya Ramu Bala Rabiu. Na yi makarantar model a matakin raino da matakin firamare na wuce makarnatar sakandare a makarantar da ake kira Crescent international daga nan kuma na wuce jami`ar Bayero inda na karanta harkar ƙididdigar kuɗi (Accounting) daga digiri na farko har zuwa na uku duk a Bayero Kano kasan kuma ina yi ina koyarwa ne a wannan fanni a BUK.
Bayan buɗe jami`ar Khairun ne akace inzo in bada gudunmawa a matsayin mamba a kwamatin amintattu wato BOT a KHAIRUN toh daga nan ne na dakatar da aikina na wucin gadi a jami`ar Bayero ta Kano. Daga baya kuma sai naga ya dace inzo in shiga har aiki tsundum a jami`ar toh shine kuma na bar Bayero na dawo nan Jami`ar KHAIRUN da aiki har na zama Bursar wakiliyar kuɗi.
Bisa la`akari da tarihinki na karatu ya zaki bayyana muhimmancin ilimin `ya`ay mata?
A gaskiya ilimin `ya mace na da muhummanci ba wai dan a kaina zan bada misaliba ga ba daya jama`a zanyi bayani kamar yadda na fahimta ni a gani na da fahimtata ta ilimi, ilimin `ya mace ya fi muhummanci akan na namiji domin `ya mace ita ce makarantar farko ga al’umma. Tun daga haihuwar ‘ya’yanta za ta fara koyar da su, har su fara wayo sannan ta kai su ga makaranta. Bayan kai su makaranta ma ba tsayawa za ta yi ba, asalima har girma akan kiyarwata suke. Kaga kuwa idan aka yi rashin sa’a uwa ba ta da ilimi musamman na addini ba shakka za a samu tasgaro. Kuma abinda nake so masu karatun wannan jarida zu sani, shi fa ilimi ba ana yin sa ba ne kawai don a samu aiki ba, shi ilimi na addini da na zamani na da matuƙar muhimmanci musamman ga uwa. Idan aka ce ka ɗauki misali da gidan da mace mai ilimi take jagoranta da kuma wanda marar ilimi ke tarbiyya tabbas za ka tarar da tarbiyyar gidan da akwai ilimi za ta bambanta da gidan da babu ilimi.
Idan na fahimce ki darajar ilimin mace ya wuce a yi don ta yi aiki kawai?
Tabbas haka nake nufi domin akwai iyaye da dama da suke cewa su ya’yansu mata ba za su yi ilimin zamani ba tunda ba aiki za su yi ba. A’a zai fi kyau a yi ilimin don matsayinsa na ilimi, shi aiki kuma wani abu ne daban.
Na ga Majalisar ɗinkin Duniya na bikin ranar ilimin mata ta duniya duk shekara. Me za ki ce a matsayinki ta mai digiri da digirgir PHD?
Toh gakiya wannan rana tsna da muhimmaci domin zata ƙsrfafa gwiwar mata su tashi su nemi ilimi saboda muhimmancinsa kuma zai yi kyau a hukumomi da ƙungiyoyi da sauran masu ruwa da tsaki da ɗaukacin al’umma su tashi tsaye wajen sauƙaƙa abubuwa da za su sauƙaƙa samun ilimin mata da sauran al’umma.
Kin yi karatu har zuwa digiri na uku gashi kin yi harkar koyarwa. Wane ƙalubale mata ke fuskanta a harkar karatu?
To, a matsayina ta malamar jami`a tsawon shekara 12 zuwa 13 na gano mata na da babban kule ko ƙalubale a wajen karatu kodai kafin aure ko bayan sun yi aure, duk kana samu matsala ta farko ta gida kamar guda biyu za ace matsala ta farko shine idan aka samu wani uba ko wakilin yarinya ne ke son karatu kuma uwa ba ta so `yarta ta yi karatun ko kuma uwa tana so uba ba ya son karatun to fa akan samu matsala indai wani ba ya so a cikinsu mahaifiya ko mahaifi to fa ana samun matsala duk wanda ba ya so a yi karatun ba zai bada gudunmawa ba koda kuwa ta ƙarfafa gwiwa ne wannan babban ƙalubale ne a neman ilimin `ya`ya mata. Haka abu na gaba a ƙalubalen karatun mata a jami`a shine a gidan aure zaka ga cewa wani wanda zai auri yarinya ya amince rimi-rimi in sun yi aure za su cigaba da karatu amma mafiya yawa daga baya na juya baya su ce ba ruwansu da karatu idan ma wani ya yadda za a yi sai ka ji ya ce ba zai ɗau nauyi ba koda kuwa yana da dama balle kuma wanda bai da dama sai kaga hatta hidindimin gida sai ta yi komai kafin ta tafi makaranta, wani hatta yaran da matar ta haifa sai ya ce sai ta tafi dasu makaranta domin bai yadda akaisu ko ina ba da dai sauran matsaloli da na samu bayani daga wasu ɗalibaina a yayin da suka samu kamsu a ciki suna neman shawara ko mafita daga wajena sai in ba su shawarwari ta mafita akan cewa su yi haƙuri wata rana sai labari, sakamakon irin waɗannan matsaloli sai kaga ana yin karatun ba nutsuwa saboda ƙalubale sakaamakon rashin tallafi wanda dole sai an haɗa karatun da neman yadda za a yi karatun na hidindumun kuɗin da makaranta ke buƙata wanda hakan yakan kawo faɗuwa da maimaita aji a wajen karatu musamman a jami`a.
Dr. Naja’atu, wacce matsala ko ƙalubale kika samu a lokacin karatunki na jami`a?
To, ni gaskiya ban samu matsala a karatuna ba domin abinda ya jawo na shiga jami`a shine yadda sakamakona ya yi kyau na kammala sakandire domin ni ce mace ta farko a zuri`ar Sheik Muhammad Rabi`u da ta shiga jami’a saboda a lokacin samakona na cin jarrabawa 100 bisa 100 domin duk darusa tara duk AA na samu, da wannan ce mahaifiyata da abokan shawara suka nemi shawo kan mahaifina kan ya bar ni na ɗora karatu zuwa jami’a, duk da cewa mata ba sa wucewa a gidanmu kasancewar iyayenmu malamai ne da suka duƙufa wurin yi wa ƙur’ani hidima, duk da haka cikin sa’a mahaifina malam Bala ya amince mani zuwa jami’a, amma fa da sharaɗin likitanci zan karanta. To duk da mun fahimci yana nufin ɓangaren lafiya zan yi karatun kai, kuma a ka amince da hakan duk da ba hakan Allah ya tsara ba. Wannan dai shi ne dalilin shiga ta shiga ta Jami’a bisa yarda da amincewar iyayenmu. Hakan kuwa zan iya cewa babbar nasara ce gare ni na zama ta farko a mata a gidanmu da ta buɗe fagen cigaba da karatu.
Wacce nassara ce kika fi alfahari da ita a rayuwa?
Nasarori ba wanda ba mu gani ba domin ka shiga jami`a ka gama lafiya ma babban nassara ce, har a gama PHD babbar nassara ce domin ban taba mai-maita aji ba duk inda sakamakon jarrabawa ya fito bani da wata matsala saboda haka digiri na ɗaya da na biyu da na uku ban taɓa samun sakamako mafi ƙanƙanta ba duk masu daraja ne kuma amatsayina ta matar aure mai haihuwa da renon `ya`ya kamar yadda nake yawan gayawa ɗalibai na dawainiyar da hidindumun aure ba su hana ni karatu ba. Wannan nasara ce babba kuma wannan nasarar ce ta sa na zama Dakta ta ilimi ba ta lafiya ba. Duk da haka ubangiji ya karɓi maganar maaifina, shi ya sa da na kammala sai da muka yi kuka ni da mahaifiyata, yau na zama dakta kamar yadda ya ce, amma ba ya raye ya gani. Sai kuma muka bi shi da addu’ar nema masa rahma.
Kin ambaci aure da haihuwa a lokacin da kike karatu da aiki a jami`a. Yanzu ’ya’ya nawa ne ki ke da su?
Ubangiji Maɗaukakin Sarki ya azurta ni da `ya`ya guda 3 namiji ɗaya mata biyu. Babbar `yata an aurar da ita yanzu haka tana gidan miji ƙaninta yana jami`a yanzu haka. Ta uku ƙaramar tana makarantar firamare a wannan lokaci.
Yaya ya kamata mace ta zama bayan ta yi ilimi mai zurfi domin bayanai sun nuna cewa wasu mata da dama idan sun yi ilimi mijinta sai dai haƙuri rayuwarsu ta kan zama kamar ta gwauro?
Rashin tarbiyya ne ke sa rashin biyayya ga miji ko na gaba da kai amma dai ba karatu ba mai karatu da tarbiyya ba zai haka ba domin dole ne mace ta zama mai biyayya ga mijinta da kuma kame kanta a wajen aiki da sauransu. Don haka rashin tarbiyya ko rashin kamun kai da duk wani abu na ƙi ga mace ba karatu ke kawo shi ba. Akan samu wadda ba ta taɓa shiga aji ba ma kuma ta zama marar biyayya ga mijinta, kenan ba karatun ba ne matsala. Ita mai ilimi idan tana da tarbiyya saidai ta ƙara girmama shi da yin mu’amala da shi cikin kyakkyawa mu’amala wadda shari’a ta amince da ita.
A ƙarshe me ki ka fi ƙauna kiyi a rayuwarki?
Idan da abinda zance na fi kauna ko sha`awar yinsa a rayuwata shine karanta littafi ko na addini ko na zamani shiyasa kwamfuyuta da littafi sun zama kamar aminaina na kusa sai kuma harkar tafiye-tafiye shima ina da sha`awa sosai. Mun gode wa Ubangiji.
