Ɗan hidimar ƙasa ya rasu sanadin artabu tsakanin sojoji da ‘yan fashi a Abuja

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Wani mai wa ƙasa hidima mai suna Abdulsamad Jamiu ya rasu bayan ya shiga tsakiyar musayar wuta tsakanin ‘yan fashi da jami’an tsaro a yankin Dei-Dei da ke Abuja. Lamarin ya faru ne da asubahin ranar 25 ga Afrilu, 2026, a Shagari Estate, lokacin da sojoji suka amsa kiran gaggawa kan harin fashi.

A cewar rundunar sojin Najeriya, jami’ansu na sintiri ne lokacin da suka isa wurin kuma suka gamu da harbin bindiga daga ‘yan fashin da ke ƙoƙarin tserewa. Wannan ya janyo musayar wuta mai tsanani tsakanin sojojin da maharan, inda a cikin rikicin Abdulsamad ya samu rauni mai tsanani sakamakon harbin bindiga.

Duk da ƙoƙarin da jami’an tsaro suka yi na kare mazauna yankin da taimaka wa waɗanda abin ya shafa, an tabbatar da mutuwar Abdulsamad daga baya. Rundunar Guards Brigade ta jajanta wa iyalansa da hukumar NYSC, tare da bayyana lamarin a matsayin abin takaici, sannan ta ce an fara bincike domin gano yadda al’amarin ya faru. An ajiye gawarsa a asibitin Kubwa General Hospital.

By ukarofi