Kano: ‘Yan daba sun raunata mutane da sace kayayyaki a kasuwar Farm Centre

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Al’umma sun shuga firgici a cikin garin Kano a yau Litinin, yayin da wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun kai hari a shahararriyar kasuwar sayar da wayoyin hannu ta Farm Centre da tsakar rana, lamarin da ya yi sanadin raunata mutane da dama da sace kayayyaki masu daraja.

Rahotanni sun ce maharan sun afka wa kasuwar ne, wadda jama’a da dama ke hada-hada, inda suak firgita ‘yan kasuwar da kwastomomi da makamai masu kaifi tare da karɓe iko da wani sashen yankin.

A ruwaito cewa, a sashen Yoyo Plaza, sun riƙa dukan mutane tare da amfani da makaman nasu wajen tsorata jama’a.

Shaidu sun ce an kuma ƙwace wayoyin hannu da sauran kayayyaki daga hannun ‘yan kasuwa da masu wucewa a wajen.

Wata majiya daga cikin ‘yan kasuwar ta shaida wa ‘yan jaridar cewa, ana zargin wasu daga cikin maharan sun fito ne daga wani taron siyasa da aka gudanar a kusa da kasuwar, kodayake babu wata hujja daga hukumomi da ke tabbatar da hakan.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa shigar gaggawar jami’an ‘yan sanda ɗauke da makamai ya taimaka wajen tarwatsa maharan, inda suka daƙile rikicin kafin ya rikide zuwa babbar tashin-tashina.

Zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, babu tabbacin adadin waɗanda suak jikkata, saidai an ruwaito cewa wasu mutane sun samu raunuka yayin faruwar al’amarin.

Haka kuma, ƙoƙarin ji ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano bai yi nasara ba don bai amsa kiran waya ko sakon kar ta kwana da aka aike masa ba.

By Babaji