
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani abin tausayi ya riski jama’a a ƙauyen Gako da ke Ƙaramar Hukumar Riyom ta Jihar Filato a daren Lahadi wayewar Litinin, inda wasu ‘yan bindiga suka halaka wani fasto da makusantansa uku a wani sabon hari a yankin.
An ruwaito cewa waɗanda aka halakan sune; Reberen Ayuba Choji, matarsa Chundung Ayuba, da kuma ‘ya’yansu biyu, Cyril da Endurance Ayuba, waɗanda suai rasu a lokacin da ‘yan bindigar suka yi ta harbe-harbe na kan mai-uwa-da-wabi da misalin ƙarfe 11 na dare.
Mazauna yankin sun bayyana cewa, sun tsinci kansu a halin firgici da rikicewa na harbin bindiga a ƙauyen, wanda ya tilasta musu tserewa zuwa juji mafi kusa da su domin neman tsira.
Wata ‘yar ƙauyen mai suna Martha Dalyop da ta gana da manema labarai ta wayar hannu, ta ce harin ya gigita yankin baki ɗaya saboda ƙarfin harbe-harben maharan.
Ta bayyana cewa, cigaba da kai hare-hare a yankin ya sanya al’umma zama cikin halin ɗar-ɗar, waɗanda da dama daga cikinsu ba sa iya kwana a gidajensu ko zuwa gonakinsu.
Sakataren yaɗa labaran Ƙungiyar Matasan Birom, Rwang Tengwong, ya ce maharan suna aiki ne a ƙungiyance da salo iri guda na harar ƙauyuka da wasu yankunan jama’a.
A cewarsa, su kan rabu a wasu lokuta yayin kai farmaki, inda a lokacin da wasu ke farmakar jama’a, wasu kuwa lalata gonaki suke, sai kuma wasu su tare hanyoyin da suka san mutane suna bi su tsira.
