
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyya mai mulki APC, ta fitar da sabon jaddawali da tsare-tsaren harkokinta na zaɓen 2027.
Hakan na ƙunshe ne a wata takarda da Sakatarenta na Shirye-shirye na Ƙasa, Sulaiman Muhammad Argungu ya fitar a yau Litinin.
Daga cikin ababen da aka sauya a jaddawalin akwai lokaci, tantancewa, ɗaukaka ƙara da zaɓukan fidda gwani da dai sauransu yayin da aka bayar da umarnin sayar da fom da kuma amince wa asusun da za a biya kuɗaɗen mallakar su.
A cewar wannan jaddawali, za a gudanar da zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa a ranar Asabar, 23 ga watan Mayu, Sai na gwamnoni, wanda za a yi a ranar Alhamis, 21 ga Mayu, 2026.
Hka kuma, za a gudanar da na ‘yan majalisar dokokin jihohi a Laraba, 20 ga Mayu, sai na majalisar dattawa a 18 ga Mayu da kuma na majalisar wakilai a Juma’a, 15 ga Mayu.
Jam’iyyar ta kuma jaddada cewa, za a ta sayar da fom ɗin takarar shugaban ƙasa ne akan ₦100,000,000, sai na gwamnoni akan ₦50,000,000.
Masu neman tsaya wa takarar sanata kuwa, za su sayi fom ne akan ₦20,000,000. Na majalisar wakilai kuma akan ₦10,000,000, sannan sai ₦6,000,000 ga na majalisun dokokin jihohi.

