‘Yan bindiga sun kashe mutane 11 a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

‘Yan bindiga sun kashe mutane 11 tare da raunata mutum 2 a ƙauyen Gurbi da ke ƙaramar hukumar Ƙankara na jihar Katsina.

A wata takardar sanar wa ɗauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce haɗin gwiwar jami’an tsaro ƙarƙashin DPO na Ƙanƙara sun kai ɗauki a ƙauyen.

Sai dai acewar sa bayan da yan bindigan suka hango jami’an tsaron sai suka ranta a na kare.

DSP ya bayyana cewa a halin yanzu zaman lafiya ya dawo a ƙauyen a dai dai lokacin da jami’an tsaro suka shiga farautar ‘yan bindigan.

Ya ce tuni yan sanda suka miƙa gawarwakin ga iyalan su domin yi masu sutura su kuma waɗanda suka sami raunuka an garzaya da su asibiti.

‘Yan sandan sun yi kira ga al’ummar yankin da su cigaba da hidimar na yau da kullum a yayin ka kwamishinan ‘yan sanda a Katsina ya bada umurnin ƙara jibge jami’an tsaro a ƙauyen.

Rundunar yan sanda a cewar DSP Abubakar Sadiq ta miƙa ta’aziya ga iyalan waɗanda aka kashe tare da tabbatar masu da cewa yan sanda na nan na ƙoƙarin gano maɓoyar.

By ukarofi