ADC-PDP: Kotun ƙoli ta tabbatar da David Marka, ta kori Turaki

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kotun ƙoli ta soke umarnin nan na “status ƙuo ante bellum”, wato dawo da komai yadda yake a da, wanda Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta bayar game da rikicin shugabancin Jam’iyyar ADC.

Wannan hukunci ya maida shugabancin da David Mark ke jagoranta kan madafun iko, bayan da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ta soke sunayensu a baya.

A cikin hukuncin da alƙalan kotun guda biyar suka yanke baki ɗaya a ranar Alhamis, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Mohammed Lawal Garba, kotun ta bayyana cewa umarnin da Kotun ɗaukaka ƙara ta bayar ba shi da muhimmanci. Haka zalika, kotun ƙolin ta bayyana cewa an shigar da ƙarar kan batun “ikon shari’a” ne bisa wani umarni na musamman ba tare da neman izini daga kotun ɗaukaka aara ba tun da fari.

A wani ɓangaren kuwa akasin haka aka samu, inda Kotun ƙoli ta Nijeriya ta haramta Babban Taron ƙasa na Jam’iyyar PDP da aka gudanar a birnin Ibadan, Babban Birnin Jihar Iyo, tare da rushe tsagin shugabancin jam’iyyar a ƙarƙashin Barista Kabiru Tanimu Turaki, wanda aka zaɓa a wajen taron.

A yayin da take yanke hukuncin, wanda ya samu rinjayen mutum uku cikin alƙalai biyar, Kotun ƙoli ta bayyana cewa ɗaukaka ƙarar da Tsagin Tanimu Turaki ya yi ba shi da hujja, don haka suka yi watsi da shi.

Yayin da yake karanta hukuncin kotun a ranar Alhamis, Mai Shari’a Stephen Adah, ya bayyana cewa alƙalai ukun da suka yi rinjaye sun bayyana cewa taron da tsagin Turaki na Jam’iyyar ya gudanar a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba ya saba da umarnin Mai Shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da kuma hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara da suka hana gudanar da taron.

Daga nan suka soke ɗaukaka ƙarar da tsagin na Turaki ya shigar, inda suke taƙaddama da ɓangaren Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyeson Wike, kan shugabancin Jam’iyyar.

Alƙalan Kotun Kolin sun soki tsagin Kabiru Tanimu Turaki na jam’iyyar game da sake shigar da kara a wata kotu mai daraja daidai da wadda ta batar da umarnin, maimakon zuwa Kotun ɗaukaka ƙara.

Don haka ta bayyana matakin a matsayin wasa da tsarin shari’a, suna masu ƙarawa da cewa duk mai shigar da ƙara da ya kuskura saɓa wa tsarin kotu, ya kuka da kansa.

Da wannan hukunci, tsagin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da ke ƙalubalantar taron Ibadan da Shugabancin Turaki, ya samu nasara

By ukarofi