Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya gabatar da takardar shi ta shedar tsayawa takara karo na biyu domin neman zarcewa a kan kujerar Gwamnan jihar Katsina.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da shirye-shiryen siyasa ke ƙara kankama gabanin zaɓukan da ke tafe na shekarar 2027.
Gabatar da shedar ya nuna ƙudurin gwamnan na ci gaba da jagorantar jihar tare da cigaba da kawo manufofi da shirye-shiryen ci gaba da ya fara, musamman a fannoni kamar tsaro, ilimi da bunƙasa tattalin arziki.
Waɗanda suka halarci gabatar da fom din sun hada da shugaban jam’iyyar APC, Dr. Bishir Gambo Saulawa, shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Katsina da sauran su.
Haka suma sakamakon sasanci, Sanata Abdul’aziz Musa Yar’adua da Sanata Muntari Dandutse sun sami tikiti na ƙara tsayawa takarar kujerar da suke kai a zaɓen 2026.
