Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa matatun mai na gwamnati a Nijeriya ba za su sake yin aiki yadda ya kamata ba.
Manhaja ta rawaito cewa Obasanjo ya ce ya dade ya na da wannan ra’ayi duk da sukar da ake masa.
Bayan watanni uku da hawa mulki, Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ce matatar mai ta Port Harcourt za ta fara aiki nan da Disamba 2023, bayan kammala gyaran da aka ba kamfanin Maire Tecnimont SpA tare da NNPC.
Sai dai Obasanjo ya ce ya riga ya san matatun ba za su gyaru ba, bisa bayanin da ya samu daga kamfanin Shell lokacin da ya ke shugaban ƙasa.
Ya ƙara da cewa tsarin haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu (PPP) ne mafi inganci, yana bada misalin kamfanin Nigeria LNG Limited, inda kamfanoni masu zaman kansu ke da kaso mafi yawa (51%), gwamnati kuma na da 49%, kuma aikin yana tafiya yadda ya kamata.
Obasanjo ya kuma bayyana cewa lokacin da yake shugaban ƙasa, ya nemi kamfanin Shell ya karɓi gudanar da matatun mai, amma suka ƙi
Sai dai kuma fadar shugaban ƙasa ta maidawa Obasanjo martani, inda Mai taimakawa shugaban ƙasa kan yaɗa labarai, Tope Ajayi, ya ce Obasanjo ba injiniya ba ne, don haka bai kamata ya yi irin wannan hasashe ba.
Ya ce gwamnati na bin rahoton injiniyoyin da ke aiki a matatun, kuma ya kamata a jira a gani.
