Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Tsohon kwamishinan kasuwanci na Jihar Kano, Shehu Wada Sagagi, ya bayyana cewa jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya kammala shirye-shiryen ficewa daga jam’iyyar ADC.
Sagagi ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da kafar yaɗa labarai ta Arewa Update, inda ya ce matakin ficewar ya samo asali ne sakamakon rikicin shari’a da ya dabaibaye jam’iyyar.
A cewarsa, ci gaba da rikice-rikicen cikin gida da kuma takaddamar da ke gaban kotu sun sanya shugabannin tafiyar ganin ya dace su sake nazarin makomarsu ta siyasa
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, jam’iyyar ADC ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da wannan ikirari, haka kuma Rabiu Musa Kwankwaso bai fito fili ya tabbatar ko ya musanta batun ba.
