Daga ABUBAKAR A. BOLARI, Gombe
Shugabar mata ta tafiyar ƙungiyar ci gaban matasa magoya bayan ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya a mazabar Gombe, Kwami da Funakaye, Wunan Anthony, ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Zakariya Jidda, inda ta ce shi ne zaɓin da ya dace domin wakiltar al’ummar yankin a zaɓen 2027.
Wunan Anthony ta bayyana haka ne yayin da take zantawa da manema labarai a Gombe, inda ta jaddada cewa matasa da mata a yankin sun yanke shawarar tsayawa tsayin daka wajen ganin Zakariya Jidda ya samu tikitin takara a ƙarƙashin jam’iyyar APC tare da lashe zaɓe.
A cewarta, Zakariya Jidda matashi ne mai kishin ci gaban al’umma, wanda ya daɗe yana tallafawa jama’a tun kafin ya fara harkokin siyasa.
Ta ce irin wannan hali ne ya sa suke ganin idan aka ba shi dama, zai kawo sauyi mai ma’ana a rayuwar al’ummar mazaɓar.
“Mun san irin ƙoƙarin da yake yi wajen taimakon jama’a, musamman matasa da mata. Wannan ne ya sa muka yanke shawarar cewa shi ne ya dace mu mara wa baya. Muna da yaƙinin cewa idan ya samu tikiti a APC, zai iya lashe zaɓe cikin sauƙi,” inji ta.
Ta ƙara da cewa ƙuri’un mata a yankin na hannunsa ne, tana mai tabbatar masa da cewa za su shiga lungu da saƙo domin wayar da kai da kuma yaƙin neman zaɓensa.
Ta ce mata a Gombe, Kwami da Funakaye sun shirya tsaf domin ganin sun taka rawar gani wajen tabbatar da nasararsa.
Wunan Anthony ta kuma yi nuni da cewa tarihin yankin ya nuna cewa ba kowane ɗan majalisa ne ya taɓa kai irin gudunmawar da Zakariya Jidda ke bayarwa ba, musamman duba da cewa shi ɗan kasuwa ne ba mai muƙamin siyasa ba yake gudanar da ayyukan jin ƙai da raya al’umma.
Ta ce irin wannan gudunmawa ce ta sa Mai Martaba Sarkin Funakaye, Alhaji Yakubu Muhammad Kwaranga, ya karrama shi da sarautar Jagaban Matasan Funakaye, alamar amincewa da irin rawar da yake takawa wajen cigaban yankin.
Sai dai ta yi kira gare shi da cewa idan ya samu nasarar zama ɗan Majalisar Wakilai, ya fi mayar da hankali wajen tallafa wa mata da kayan sana’o’i da shirye-shiryen dogaro da kai, domin inganta rayuwarsu.
“Mu mata muna da muhimmiyar rawa a cikin al’umma. Don haka muna roƙon sa da ya ba mu kulawa ta musamman ta hanyar samar mana da tallafi domin mu dogara da kanmu,” in ji ta.
Ta kammala da cewa lokaci ya yi da al’ummar yankin za su zaɓi shugabanni masu kishin gaskiya da ci gaban jama’a, tare da jaddada cewa Zakariya Jidda na ɗaya daga cikin irin waɗannan mutane da ake buƙata a wannan lokaci.
