Surikin Dangote ya bada shawarar soke ranakun hutu a Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Jamil Abubakar, surukin attajirin ɗan kasuwa Aliko Dangote, ya tayar da muhawara a kafafen sada zumunta bayan ya ba da shawarar cewa ya kamata a soke dukkan ranakun hutu a Nijeriya domin ƙara yawan aiki da bunƙasa tattalin arziki.

A wani saƙo da ya wallafa, Jamil ya bayyana cewa Nijeriya na baya sosai idan aka kwatanta da sauran ƙasashe, don haka akwai buƙatar ƙara ƙaimi domin cike giɓin da ke akwai.

Ya ce idan aka rage ko aka soke hutun gwamnati da na ƙarshen mako, hakan zai bai wa jama’a damar mai da hankali sosai kan aiki da ci gaban ƙasa.

Sai dai ya ƙara da cewa za a iya ware rana ɗaya kacal a kowane mako domin hutu, kafin a koma aiki yadda ya kamata.

A cewarsa, “Ya kamata a soke duk ranakun hutu a Nijeriya. Mun yi baya sosai, dole mu dage. A gaskiya ma, har hutun ƙarshen mako ya kamata a soke. Kowa ya samu rana ɗaya kawai don hutu, sannan a ci gaba da aiki. Wannan yawan hutu ba tare da kuɗi ba, wa yake amfana?”

Ra’ayinsa ya janyo martani mabambanta daga jama’a, inda wasu ke ganin hakan na iya taimakawa wajen ƙara yawan aiki, yayin da wasu ke ganin hakan zai taƙura rayuwar ma’aikata da jin daɗinsu.

A gefe guda, a ranar 20 ga Afrilu 2026, Aliko Dangote ya sanar da naɗa Jamil Abubakar a matsayin Daraktan Gudanarwa na Sashen Ababen More Rayuwa da Sufuri a kamfanin Dangote.

Jamil, wanda ya auri Fatima Dangote, ya yi fice a harkar jiragen sama, inda ya kwashe sama da shekaru 14 yana aiki a kamfanonin jiragen sama daban-daban, ciki har da Azman Air da NG Eagle Airlines, inda ya riƙe muƙamin babban matuƙin jirgi.

Baya ga harkar jiragen sama, yana da gogewa a fannin zuba jari da shugabanci, inda ya taɓa riƙe muƙamai a kamfanoni da hukumomi daban-daban na gwamnati da masu zaman kansu.

A Nijeriya, ana da ranakun hutu da dama a kowace shekara, ciki har da Sabuwar Shekara, Sallah Babban da ƙarama, Good Friday, Ranar Ma’aikata da kuma Ranar ’Yancin Kai, waɗanda ake ɗauka a matsayin muhimman ranaku na ƙasa da addini.

Duk da haka, shawarar Jamil ta sake buɗe muhawara kan daidaita tsakanin aiki, hutu da jin daɗin rayuwa, musamman a ƙasar da ke fama da matsalolin tattalin arziki.

By ukarofi