
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makaranta (JAMB), ta sanar da cewa za ta gudanar da taron manufofin shiga jami’o’i na shekarar 2026 a ranar 11 ga Mayu, 2026 a Abuja.
JAMB ta ce, za ta yi hakan ne domin tantance mafi ƙarancin makin UTME (cut-off mark) da kuma sabbin ƙa’idojin shiga manyan makarantu a faɗin ƙasar.
A wata sanarwa da Kakakin JAMB, Fabian Benjamin, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce taron zai haɗa da manyan masu ruwa da tsaki a fannin ilimi, inda Ministan Ilimi, Tunji Alausa, zai bayyana muhimman sababbin tsare-tsare da manufofin da za su jagoranci tsarin bayar da guraben karatu a jami’o’i, polytechnic da kwalejojin ilimi na Nijeriya.
Haka kuma, sanarwar ta bayyana cewa, taron zai shirya hanyoyin da za a bi wajen samun gurbin karatu da kuma ƙarfafa buƙatar manyan makarantu su bi tsare-tsaren da aka amince da su.
Kazalika, Benjamin ya ce zaman zai bayar da dama ga masu ruwa da tsaki na su yi nazari game da matsalolin da ke shafar samun gurbin karatu da kuma jaddawalin kakar karatu ta gaba.
