
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sa’o’i bayan tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso sun shiga jam’iyyar NDC a hukumance, an sabon rikici akan zargin ta da rashin kiyaye sharuɗɗan rajista daga Hukumar Zaɓe, INEC.
Hakan na zuwa ne a lokacin da jagoran jam’iyyar ADA, Umar Ardo ya ƙalubalanci sahihancin rajistar NDC a kotu, inda ya zargi jam’iyyar da gaza cika sharuɗɗan dokokin ƙasa da tsare-tsaren kafin amincewa da ita a hukumance.
An samu wannan al’amari ne jim-kaɗan bayan shigar Obi da Kwankwaso cikin NDC a hukumance, inda aka na su katinan zama mambobi a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja.
Duk da cewa a watan Fabrairun 2026, INEC ta ce jam’iyyu biyu daga cikin 171 da suka nemi a tabbatar da ta yi wa rajista, Shugaban hukumar Joash Amupitan, ya ce jam’iyyar DLA ce kaɗai aka yi wa rajista.
Dakta Umar Ardo, ya bayyana aniyarsa ta gurfanar da jam’iyyar a gaban kotu, inda yake zargin cewa an karya ƙa’idoji da dokokin cikin gida na jam’iyyar wajen wannan mataki.
Rahotanni na cewa lamarin na iya ƙara haifar da rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar, yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.
