Zaɓen 2027: An yi kira ga matasan Katsina su guji bangar siyasa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban ƙungiyar cigaban Funtua kwamred Mannir Suleiman yayi kira ga matasa a faɗin jihar Katsina musamman yankin Funtua da su guji bangar siyasa domin kyautata rayuwar su da mutuncin su.

Kwamred Suleiman yayi wannan kira a Katsina a wata hira da manema labarai inda ya nuna damuwarsa kan yadda matasa suka gujewa karatu da sana’o’i suka koma bin ‘yan siyasa.

Ya ce wajibi ne matasa su tashi tsaye wajen nema na kansu makamai dubu da halin matsin tattalin arzikin ƙasar.

Ya yaba wa gwamna Dikko Raɗɗa kan kafa dokar ta ɓaci kan ƙauraye da bangar siyasa da yace zai taimaka wajen inganta tsaro da tsaftace harkokin siyasa a jihar.

Haka kuma ya yaba wa gwamna Dikko Raɗɗa da ya ɓullo da shirin kafa cibiya na koyon sana’o’i a duk ƙananan hukumomi 34 da ke faɗin jihar.

Kwamred Suleiman sai yayi kira ga matasa da su mai da hankali wajen koyon sana’o’i a waɗannan cibiyoyi wanda sauran sun kammala gwamnatin za ta tallafa masu da jari da zai taimaka masu su fara sana’a.

“Bangar siyasa babu abinda ke haifar wa sai zubar da mutunci, jefa rayuwa cikin haɗari da shaye shaye a tsakanin matasa,”inji Mannir.

“Da wannan kotun tafi da gidan ka da gwamna Raɗɗa ya kafa ya rage ga ku matasa in kunne ya ji jiki ya tsira,”Kwamred Suleiman ya ce

By ukarofi