
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Bello El-Rufai, wanda ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ne, ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa ta adawa, wato ADC.
Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas ya karanta takardun sauya sheƙar nasu yayin da majalisar ta koma zaman aiki a yau Alhamis.
Tajudeen Abbas ya bayyana ce Bello El-Rufai, wanda ke wakiltar mazaɓar Kaduna ta Arewa, ya koma jam’iyyar ADC ne tare da wasu ‘yan majalisar biyu na jam’iyyar PDP daga Jihar Kaduna, wato Umar Ajilo da Suleiman Yahaya Richifa.
Ya kuma sanar da sauya sheƙar Kamilu Ado, ɗan majalisa daga Kano na ADC zuwa jam’iyyar NDC.
Haka kuma, kakakin ya sanar da ficewar Joshua Obika, mai wakiltar mazaɓar AMAC/Bwari ta Abuja daga APC zuwa NDC.
‘Yan majalisar da suka sauya sheƙar sun danganta matakin nasu da rikice-rikicen cikin gida da rashin tabbas da ke addabar tsofaffin jam’iyyun nasu.
