
Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana cewa ya ji kiraye-kirayen da ake yi masa na ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027, yana mai cewa zai yi shawara sosai kafin ɗaukar matsaya.
Jonathan ya bayyana hakan ne yayin da wasu matasa sukayi zanga zanga a ofishin sa dake abuja suna neman kuma suka buƙace shi da ya sake tsayawa takara, inda ya ce:
“Ina gode muku da irin sha’awar da kuke nunawa kan Najeriya. Da ba ku da kishin ƙasa, da ba ku zo nan ba. ‘Yan ƙasa masu kishin ƙasa ne kawai suke gina ƙasarsu, marasa kishin ƙasa kuwa suna lalata ta sannan su kwashe kuɗi zuwa ƙasashen waje domin jin daɗin rayuwa.”
Ya ƙara da cewa babban abin da Najeriya ke buƙata shi ne zaman lafiya, tare da kira ga al’umma da su ci gaba da fafutukar tabbatar da sahihin zaɓe mai cike da lumana.
Tsohon shugaban ƙasar ya kuma nuna damuwa kan yadda masu kaɗa ƙuri’a ke ƙauracewa zaɓe a Najeriya, yana mai cewa ƙasar na daga cikin wuraren da ake fama da ƙarancin fitowar masu zaɓe a duniya.
Dangane da batun takara kuwa, Jonathan ya ce:
“Kun zo yau kuna roƙona da na tsaya takara. Na ji ku. Takarar shugaban ƙasa ba wasan kwamfuta ba ce. Zan yi shawara sosai.”
Kalaman nasa na cigaba da haifar da ce-ce-ku-ce a fagen siyasar Nijeriya yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.
