Rashin tsaro na barazana ga zaɓukan 2027, inji Shugaban INEC

Spread the love

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan ya nuna damuwa akan yadda matsalar rashin tsaro ke ƙaruwa a sassan Nijeriya, inda ya yi gargadin cewa hakan ka iya kawo cikas ga gudanar da sahihin zaɓe a 2027.

Amupitan ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai wa Sufeto Janar na ‘yan sanda, Tunji Disu, a Abuja a wani ɓangare na shirye-shiryen zaɓen, wanda ke cigaba da kusantowa.

Ya ce, matsalolin tashin hankali, maguɗin zaɓe da sayen kuri’u na daga cikin abubuwan da ke rage amincewar jama’a da tsarin zaɓe, tare da barazana ga tsaron ƙasa baki ɗaya.

A cewarsa, dole ne a yi cikakken shiri na tsaro kafin zaɓe, inda ya bukaci hukumomin tsaro su gano wuraren da ka iya zama matsala tare da ɗaukar matakan kariya domin kare masu zaɓe da jami’an zaɓe.

Haka kuma, ya jaddada muhimmancin bai wa ‘yan gudun hijira (IDPs) da masu nakasa damar kaɗa kuri’arsu ba tare da tangarda ba.

A nasa ɓangaren, Sufeto Janar na ‘yan sanda ya tabbatar da cewa rundunar za ta ɗauki matakai na musamman, ciki har da amfani da bayanan sirri da dabarun tsaro, domin magance barazanar da ke tattare da zaɓen.

Ya kuma yi gargadin cewa duk wanda aka samu da laifukan zaɓe kamar satar akwatin zaɓe, sayen kuri’u ko tsoratar da masu zaɓe, za a kama shi kuma a gurfanar da shi a gaban kotu.

By Babaji