
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Laraba Mai shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75 a kurkuku bisa laifukan cin hanci da rashawa da suka shafi ayyukan samar da lantarki na Mambilla da Zungeru, waɗanda adadinsu ya kai jimillar Naira biliyan 33.8.
Alƙalin ya ce an same shi da laifi a tuhume-tuhume guda 12 da hukumar EFCC ta gabatar akansa, sannan ya bayyana cewa hukuncin zaman gidan yarin, wanda ya kai jimillar tsawon shekaru 75.
Haka kuma, Mai shari’a Omotosho ya bayyana cewa wa’adin zaman gidan yarin zai fara ne daga ranar da aka kama tsohon ministan.
Alƙalin ya kuma umarci dukkan hukumomin tsaro da su kamo Mamman a duk inda aka same shi.
Kazalika, kotun ta bayar da umarnin a riƙe dukkan kuɗaɗe da kadarorin da aka ƙwato daga hannun tsohon ministan domin mayar da su hannun Gwamnatin Tarayya.
Har ila yau, ta umarci Mamman da ya mayar da sauran kudaden da suka rage daga cikin zargin badakalar Naira biliyan 22 da ke da nasaba da ayyukan samar da lantarki na Mambilla da Zungeru akansa.
