ASUU ta yi barazanar sake shiga yajin aiki

Spread the love

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), ta yi barazanar sake shiga yajin aiki saboda abin da ta kira da gazawar Gwamnatin Tarayya wajen cika alƙawarin yarjejeniyar da aka cimma a watan Disambar 2025.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, ASUU ta bayyana cewa har yanzu akwai matsaloli da suka hada da albashin watanni uku da rabi da aka rike, gibin albashi sakamakon amfani da tsarin IPPIS, kudaden karin girma da ba a biya ba, da kuma bashin karin albashi na kashi 25 zuwa 35 cikin dari.

Shugaban kungiyar, Christopher Piwuna, ne ya bayyana hakan bayan taron majalisar zartarwar kungiyar da aka gudanar a Jami’ar Modibbo Adama.

Ya ce rashin kulawar gwamnati kan walwalar malaman jami’o’i na kara haddasa fushi a tsakanin mambobin kungiyar, wanda ka iya jawo sabon rikicin yajin aiki idan ba a dauki mataki ba.

ASUU ta kuma ce za ta sake gudanar da taron gaggawa nan da makonni masu zuwa domin duba halin da ake ciki tare da daukar matakin da ya dace.

By Babaji