Surukar Sarki Aminu Ado Bayero ta rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Iyalan gidan Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero sun shiga alhini bisa rashin surukarsa, Hajiya Karima Lawal, wadda aka fi sani da Yayar Gandu.

Marigayiyar ta rasu ne a wani asibiti da ke Kano bayan fama da wani gajeren rashin lafiya, kamar yadda majiyoyi daga gidansu suka shaida.

Hajiya Karima ita ce mahaifiyar Hadiza Aminu Ado Bayero, wato matar Sarki Aminu Ado.

Akan haka ne aka yi ta miƙa gaisuwar ta’aziyya daga iyalai, dangi, makusantansa da sauran al’umma daga ciki da wajen Kano.

Marigayiyar ta rayuwa da ‘ya’ya tara da jikoki da dama bisa girmamawa da karamci tare da ƙoƙari wajen hidima wa al’umma.

Tuni dai aka shirya yi mata jana’iza da misalin ƙarfe 4 na yammacin yau Laraba a ƙaramar fada da ke Nasarawa.

By Babaji