Don kawo sauyi a harkar rubutu musamman wanda ya shafi mata muka kafa ƙungiyar WOW”
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Fiye da shekara guda kenan da kafa ƙungiyar marubuta ta mata zalla, wacce ake kira da Women of Words Writers Association, mai laƙabi da WOW, kuma kawo yanzu ƙungiyar ta samu cigaba sosai, da ƙaruwar mambobi, waɗanda suke ba a Nijeriya kaɗai ba har da wasu ƙasashen waje. Yadda shugabannin wannan ƙungiya suka samu nasarar haɗo kan marubuta mata na onlayin da masu ɗab’i abin a yaba ne sosai. Sai kuma ga wani abin ƙayatarwa da ƙungiyar ta ɓullo da shi a yayin bukukuwan ƙaramar Sallah da aka gudanar, inda mambobinta na sauran jihohi suka haɗa wata liyafa don taya juna murnar kammala azumin Ramadan, da buɗe sabon babi a harkar rubuce-rubucen adabi da suke gudanarwa. Wannan ne ya sa wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu ya tuntuɓi shugabar ƙungiyar Hassana Sulaiman Isma’il, domin jin dalilin su na ɓullo da wannan tsari, da kuma nasarorin da suka samu. Ku gyara zama domin karanta yadda tattaunawar su ta kasance.
MANHAJA: Ki gabatar mana da kan ki.
SANAH MATAZU: Sunana Hassana Sulaiman Isma’il, amma wasu na kira na da Sanah Matazu. An haife ni a Jihar Kano, a ƙaramar Hukumar Gwale, a Unguwar ƙofar Waika, bayan gidan Sheikh Khalifa Isyaka Rabi’u. Ni marubuciya ce, ‘yar jarida kuma ‘yar kasuwa. Na yi karatun Muhammadiya da kuma na boko, yanzu ina matsayin ɗaliba a Jami’ar Bayero ta Kano, sashen Hausa, matakin aji huɗu.
Mene ne matsayinki a ƙungiyar marubuta ta WOW?
A halin yanzu dai ni ce Allah Ya ɗorawa wakilcin shugabancin wannan tafiya zuwa wani lokaci. Ma’ana ni ce Shugaba.
Mene ne hikimar kafa ƙungiyar WOW, kuma wanne cigaba ko sauyi ta kawo a harkar rubutun adabi?
Hikimar kafa wannnan ƙungiya ta mata zalla shi ne, zaburarwa gami da kawo sauyi a harkar rubuce-rubucen adabi musamman wanda ya shafi mata. Dalilin hakan kuwa shi ne, idan muka duba muka sake hangawa ba mu da wata ƙungiya ta marubuta mata wadda ta wuce Mace Mutum. Kuma zuwa yanzu masu jan ragamar wannan tafiya iyayenmu ne kuma duk sun manyanta, akwai tarin hidindimu a kansu wanda ko da suna son wannan tafiya to, hidima ba za ta bar su ba.
Hakan ya sa mu ka ɗauki ɗamarar yin wannnan yunƙuri, kuma da shawarwarin da yawa daga cikinsu tare da ƙarfafa gwiwarsu muka cimma zuwa wannan lokaci. Daga cikin sauyin da wannan ƙungiya ta kawo na farko akwai, curewar marubuta mata waje guda musamman marubutan da suke sassa daban-daban na jihohinn Nijeriya da ma wasu ƙasasshen.
Mun kuma samar da bita akan abin da ya kamata marubuta su sake mayar da hankali akai ba wai su kafe a wuri guda ba. Kamar bitar da muka yi akan rubutun Wasan Kwaikwayo na rediyo, (Radio Drama), da bita akan rubutun muƙala, da bita akan hanyoyin da marubuci zai bi wajen cin moriyar abin da ya rubuta, da kuma bita akan wasu hanyoyi da marubuci zai bi wajen amfani da wasu manhajoji domin inganta rubutunsa.
Bayan su akwai tarin abubuwan da wannan ƙungiya ta cimma wasu kuma suna kan hanyar bayyana insha Allahu.
Daga kafuwar ƙungiyar zuwa yanzu kuna da mambobi nawa?
Daga lokacin da muka kafa wannan ƙungiya ta Women of Words Writers Association, mai laƙabi da WOW, shekara guda kenan, muna da mambobi 67, kawo lokacin wannan tattaunawa da muke yi. Mun fara kafa wannan ƙungiya ne da mutane 5, kuma a kowanne lokaci muna samun shigar sabbin mambobi. Waɗannan mambobi namu sun kasance a jihohi 13, sai wasu ƙasashe 4. Jihar Kano ta fi kowacce jiha yawan mambobi, kuma nan ne cibiyarmu take.
Bayan jihohin Nijeriya waɗanne ƙasashe ne ku ke sa mambobi, kamar yadda ki ka ambata?
Tabbas haka ne, muna da mambobi a ƙasashen Nijar, Iɓory Coast wato Kotdibuwa, sai kuma Maleshiya.
Yaya ku ke isa ga duk mambobin ku na sauran rassan, kuma ta yaya su ma za su amfana da ku?
Kasancewar cigaban rayuwa a fannoni da dama, musamman a ɓangaren sadarwa, muna isa ga mambobin mu na sauran rassa cikin sauƙi ta hanyar amfani da yanar gizo. Wannan hanya ta ba mu damar samar da duk wani abu da muke buƙata tare mabiyanmu. Kuma mukan cimma komai cikin sauƙi da aminci.
Ba da jimawa ba, mun ga yadda ƙungiyar ta gudanar da bikin ƙarfafa zumunci tsakanin mambobinta, inda aka yi liyafar bayan sallah. Yaya abin yake ne?
Haka ne. ƙungiyar mu ta samar da wannan tsari ne domin sadar da zumunci tsakanin mambobinta. Duba da cewar lokacin sallah lokaci ne mafi girma da duk wani musulmi yake alfahari da shi, wanda da yawa duk nisan inda suka je to, a wannan lokacin sukan dawo gida domin yin sallah tare da iyalinsu. Wannan ya sa muka zaɓi wannan lokaci domin ya zama na musamman wajan ƙarfafa zumunci a tsakanin ‘ya’yan ƙungiya.
Sai dai ƙarƙashin hakan ƙungiya na da manufarta na son cimma ƙarfafawa a duk wasu rassa da suke wasu jihohi, ta hanyar da zai kasance duk abin da ƙungiya take gudanarwa to, sauran mambobinta da suke wasu jihohi su ma za su kasance takwara wajen gudanar da wannan abin.
Misali, za mu iya wayar gari a Jihar Kano ana gudanar da bita akan wani abu da ya shafi rubutu, bita ta gani da ido ba bita ta kan manhajar yanar gizo. Don haka za mu so sauran mambobinmu su ma su kasance tare da mu a ranar, kuma a daidai wannan lokacin da ake gudanar da taron.
Sannan a kowacce jiha a yanzu haka muna da wakiliya dake shugabantar wannan jiha. Idan kuma muka haɗu a wuri guda gaba ɗaya kowacce mamba tana ƙasan shugabar WOW ne.
A Jihar Kaduna muna Zainab Isa, a Jihar Katsina akwai Fatima Umar, a Jihar Bauchi muna da Ramlatu Abdulrahman Manga. Sai a Babban Birnin Tarayya Abuja muna da Amra Auwal Mashi. A Zariya wacce wani ɓangare ne na Jihar Kaduna mun samar da reshe a can ƙarƙashin kulawar A’isha Yusuf Hanwa.
Sauran jahohin suma muna nan muna ƙoƙarin samar musu da wakilci, domin muna duba abu biyu ne zuwa uku. Yawan mambobin da suke jihar, yanayin jajircewar wanda zai wakilci tawagar, da kuma wasu abubuwa masu muhimmanci.
Waɗanne tsare-tsare ku ke da su nan gaba?
Muna fatan mu zo da tsare-tsaren da suka fi waɗanda muka gudanar a baya. Ciki har da gudanar da taron cikarmu shekaru biyu da kafuwa idan Allah ya ba mu iko.
Ko akwai wasu ƙalubalen da suke kawo muku cikas wajen cimma muradunku?
Rayuwa babu yadda za a ce babu ƙalubale ba, kuma wannan ƙalubalen shi ne kan iya zama matakin nasarar cimma abin da aka sanya gaba. ƙalubalen ba zai wuce datse wasu uzurorika ba, domin gudanar da wani abu da zai iya kawo cigaba a ƙungiya. Kuma ita rayuwa haka ta gada, sai ka sadaukar kake cimma abubuwa da yawa. Wata rana sai labari.
Wacce shawara za ki bai wa sauran ƙungiyoyi wajen koyi da ku?
Shawarar ba za ta wuce su kasance masu haƙuri kuma masu jajircewa tare da bibiyar ayyukan manyan mu na baya ba, sai kuma neman shawararsu akan komai, tare da ƙarfafawa waɗanda suke ƙasa da su gwiwa kan taimakon juna.
Mene ne taken ƙungiyar ku?
Kalmomin Mata Don Gina Al’umma!
