Raɗda ya umarci masu riƙe da muƙaman siyasa su koma ƙananan hukumominsu don gudanar da zaɓen fidda gwani na APC

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Raɗɗa, ya umurci waɗanda ke riƙe da muƙaman siyasa su koma yankunansu na ƙananan hukumomi don shirya wa zaɓen fidda gwani na jam’yyar APC gabanin babban zaɓen 2027.

Ya bayar da umarnin ne ajiya lokacin taron majalisar zartarwa ta Jiha da aka gudanar a sabon ɗakin taron majalisar da ke gidan gwamnatin Jihar Katsina.

Sabon ɗakin taron da aka ƙaddamar zai bada damar gunadar ayyuka ta hanyar amfani da na’urori na zamani saɓanin amfani da takardu, ɗakin taron zai kuma bada damar yin taro daga nesa, tsarin sauti mai amfani da na’ura mai kwakwalwa, da kuma dandamalin dijital wanda aka tsara don haɓaka inganci a harkokin gwamnati.

A ƙarqashin tsarin dijital, za a samar wa kowane babban jami’i wurin aiki na kwamfuta na zamani wanda aka ɗaura wa addireshin imel na gwamnati da aikace-aikacen gwamnati da ake kira e-government don inganta sadarwa, daidaituwa, da yanke shawara a tsakanin ma’aikatu da hukumomi.

Raɗɗa ya umurci dukkan waɗanda ke riƙe da muƙaman siyasa su koma yankunansu na ƙananan hukumomi nan take don kula da kuma shiga cikin ayyukan zaɓen fidda gwani kamar yadda shugabannin jam’iyya suka buƙata.

Ya jaddada buƙatar gudanar da zaɓen cikin lumana da tsari a lokacin tantance ‘yan takara.

Gwamnan ya ƙara da cewa nasarar zaɓen fidda gwani zai dogara ne akan jajircewar membobin jam’iyyar APC da masu ruwa da tsaki a matakin farko.

“Wannan wata na Mayu lokaci ne da za mu shiga cikin ayyukan jam’iyya, tun daga atisayen tantancewa zuwa zaɓen fidda gwani ga waɗanda ke son tsaya wa takara a zaɓen 2027. Muna sa ran dukkanku za ku shiga cikin shirin kuma ku tabbatar da cewa an kiyaye zaman lafiya a lokacin wannan aikin.
” in ji Gwamna Raɗɗa.

By ukarofi