
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babban malamin addinin Islama a Abuja, Sheikh Nura Khalid, ya yi kira ga maniyyatan Nijeriya na hajjin bana da su kasance masu haƙuri da lamuran hukumomin Hajji yayin da suke ƙoƙarin samar musu da yanayi mai kyau a zamansu na Makkah.
Shehin ya yi wannan kira ne a ranar Alhamis yayin gabatar wa maniyyatan jihohin Abuja da Oyo jawabi a lokacin da suka isa Makkah daga Madinah.
A cewarsa, aikin hajjin musamman a lokacin da maniyyata ke sanye da iharami na buƙatar haƙuri da juriya domin yi wa kai da Nijeriya addu’a.
Ya kuma yaba wa Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, bisa samar yanayin walwala ga maniyyata, yana mai cewa an tanadar musu da abinci mai inganci kuma wadatacce da kuma ɗakunan otal kusa da Harami.
Kazalika, shehin ya kirayi NAHCON da ta ƙara ƙaimi wajen fahimtar da hukumomin Saudiyya muhimmancin ziyartar Rawda ga ‘yan Nijeriya musamman bisa la’akari da rashin samun damar haka daga da dama daga cikinsu yayin aikin hajji.
