Daga JOHN D WADA a Lafia
Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Nasarawa Shitima Mohammed Jauro ya jaddada muhimmancin ‘yan sandan al’umma wato community policing a turance wajen samar da tsaro ƙasar Najeriya baki ɗaya yadda ya dace.
Kwamishinan ya kuma jaddada buƙatar ƙarfafa dabarun ‘yan sandan al’ummar a matsayin muhimmin kayan aiki na haɓaka tsaron ƙasa baki ɗaya a ƙasar nan.
CP Shetima ya yi wannan kiran ne a ranar Alhamis na mako da ake ciki yayin da yake karɓar baƙuncin ma’aikatan gudanarwa da na ilimi tare da ɗaliban kwamandojin babban kwas na 48 na kwalejin kwamandodi da ma’aikatan soji waɗanda suka ziyarci jihar yta Nasarawa domin yawon buɗe idon karatu.
Yawon karatun mai taken “Haɓaka haɗin kan al’umma domin ƙarfafa tsaron ƙasa,” ya mai da hankali ne kan haɓaka haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da al’ummomi wajen magance ƙalubalen tsaro da ke tasowa.
Da yake jawabi ga baƙin kwamishinan ‘yan sandan ya jaddada cewa tsaro alhakin kowa ne wanda ke buƙatar shiga tsakani na hukumomin tsaro da jama’a baki ɗaya.
Ya ƙarfafa jami’an da su rungumi ƙa’idojin ‘yan sandan al’umma yayin gudanar da ayyukansu inda ya lura cewa ƙarin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da al’umma zai taimaka wajen rage laifuka da gina amana tsakanin jama’a da ‘yan sanda da kuma ɗorewar zaman lafiya.
Shima da yake jawabi a madadin tawagar shugaban tawagar T. J. Makintosh ya gode wa rundunar ‘yan sanda ta Jihar Nasarawa bisa kyakkyawan tarba da suka yi musu sannan ya yaba wa kwamishinan kan gabatar da jawabi mai cike da ilimi mai taken “Muhimmancin ‘Yan Sandan Al’umma: Batutuwa da ƙalubale da dama ga tsaron ƙasa.”
Birgediya Janar Makintosh ya tabbatar wa kwamishinan cewa ilimi da darussan da suka samu a lokacin yawon buɗe idon karatun za a tabbatar an yi amfani da su yadda yakamata a sassan kwamandojinsu da yankunan da suke da alhaki a kai.
Ziyarar ta kasance ɓangare na shirye-shiryen ilimi da na aiki da aka tsara domin wayar da kawunan mahalarta babban kwas ɗin na 48 ga sabbin dabarun tsaro da dangantaka tsakanin farar hula da jami’an tsaro a Najeriya.
