Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Al’ummar yankunan ƙauyukan da ke tsakanin ƙananan hukumomin Kabo, Gwarzo da Karaye sun koka kan lalacewar wata muhimmiyar hanya da suka ce ta daɗe tana jefa su cikin mawuyacin hali, inda al’ummar yankin suka ce sama da shekaru 50 hanyar a lalace ta ke, lamarin da suka bayyana cewa sun gada tun daga iyayensu.
Rahotanni sun nuna cewa hanyar, wacce ta taso daga Garo ta ratsa Danejin Garo, Majema, Hayin Rimi a ƙaramar Hukumar Gwarzo, sannan ta wuce Makan Wata, Gadar Maƙera, Sarkin Ya, Jingi Sabaru, Rigarmado zuwa Gammo, Katsalle A da Katsalle B, hanyar ta haɗa al’umma da dama a ƙananan hukumomin da abin ya shafa.
A cewar mazauna yankin, sun shafe sama da shekaru 50 ba tare da an gyara hanyar ba, inda a shekarar 2011 a zamanin gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau, aka fara aikin gyaran hanyar tare da gina wasu gadoji, sun ce an yi aiki mai kyau na tsawon watanni shida kafin aikin ya tsaya, kuma gwamnatin ta ƙare ba tare da an kammala ba.
Sun ƙara da cewa daga bisani, a shekarar 2016, a lokacin Sanatan Kano ta Arewa kuma mataimakin Majalisar dattijai Barau I. Jibril Maliya an sake komawa aikin inda aka shimfiɗa tubalin gadar tare da yin titin kusan kilomita ɗaya, amma daga nan aikin ya sake tsayawa ba tare da an ci gaba ba har yanzu.
Wakilin Blueprint Manhaja a Kano ya ruwaito wasu daga cikin mazauna yankin sun bayyana cewa lalacewar hanyar na hana su zirga-zirga cikin sauƙi, musamman a lokacin damina.
“Idan muna son fita daga yankin, tafiyar kilomita ɗaya, sai mun yi zagaye mai nisa, wani lokaci har kilomita uku kafin mu isa inda za mu je, hanyar da za mu kashe dubu daya rashin gyaran hanyar ya sa sai mun kashe dubu 3,” inji Jibril.
Sun kuma bayyana cewa matsalar hanyar na shafar kasuwanci da harkokin yau da kullum, tare da yin illa ga ilimin yaransu da lafiyar al’ummarsu, inda wasu ke fuskantar asara sakamakon rashin wannan hanya.
A wani ɓangare, wasu ƙungiyoyi a yankin sun bayyana cewa sun yi ƙoƙari wajen haɗa kai domin ganin an kai ƙorafi ga hukumomi, inda suka naɗa shugabannin ƙungiya daga ƙananan hukumomin Kabo, Gwarzo da ƙaraye, domin jagorantar wannan yunƙuri.
Sai dai duk da waɗannan ƙoƙari, mazauna yankin sun ce har yanzu ba a samu wani ci gaba mai ma’ana ba, duk da cewa an taɓa samun yunƙuri a cigaba da aiki a lokacin gwamnatin Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso amma abin ya ci tura.
ƙoƙƙarin jin ta bakin hukumomin da abin ya shafa bai yi nasara ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto an tura masa saƙonni ta WhatsApp da kiran amma ba su bada amsa ba.
Al’ummar yankin na kira ga gwamnati da mataimakin gwamna, wanda suka ce ɗan yankin ne, da su ɗauki matakin gaggawa domin gyara hanyar, tare da samar da muhimman abubuwan more rayuwa kamar asibitoci, makarantu, wutar lantarki da ruwan sha mai tsafta ga al’ummar wa’yannan auyuka.
A daidai wannan lokaci da damuna ta fara kuma gangar siyasa ta fara kaɗawa, al’ummar wannan yanki na kananan hukumomi uku na matukar buƙatar wannan hanya domin samun sauƙi a rayuwarsu ta yau da kullum.
