Kungiyoyi sun gudanar da taron goyon baya da yaba wa Dakta Danjuma

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Kungiyoyi sama da ashirin ne suka gudanar da wani gagarumin taron nuna goyon baya da yabawa ga Sakataren Musamman na Gwamnan Jihar Kano, Dr. Sani ɗanjuma, bisa yadda yake tallafawa al’umma ta fannoni daban-daban na rayuwa.

An gudanar da taron ne a yankin Danladi Nasidi da ke garin Mariri a ƙaramar Hukumar Kumbotso a ranar Asabar da ta gabata.

Da yake zantawa da manema labarai, ɗaya daga cikin jagororin tafiyar, Alhaji Sunusi M. Yola, ya ce ƙungiyoyi sama da ashirin ne suka haɗu domin nuna farin cikinsu kan yadda Dr. Sani ɗanjuma ke tallafawa matasa da sauran al’ummar yankin.

Ya ce tun bayan hawansa ofis a matsayin Sakataren Musamman ga Gwamnan Jihar Kano yake kawo ayyukan ci gaba yankin, kamar samar wa matasa ayyukan yi, bayar da tallafin jari domin dogaro da kai, da kuma taimakon marayu.

Ya bayyana Dr. Sani Danjuma a matsayin jagora nagari kuma abin koyi ga ‘yan siyasa, duba da yadda yake mu’amala da al’umma ba tare da nuna bambancin jam’iyya ba.

Haka kuma ya miƙa koken al’ummar yankin ga Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, dangane da aikin wani asibiti da ke yankin wanda ya ce ya tsaya cak bayan an fara shi.

Ya kuma yi kira ga gwamnan da ya taimaka wajen gyaran titin da ya tashi daga Danladi Nasidi zuwa garin Zara, tare da bayyana fatan cewa gwamnan zai duba koken nasu.

Shi ma a nasa jawabin, tsohon Shugaban ƙaramar Hukumar Ghari, Hon. Aminu Idi Shuwaki, ya yaba wa waɗanda suka shirya taron, yana mai cewa yadda jama’a suka halarta ya nuna ƙaunar da suke yi wa Dr. ɗanjuma.

Ya ce yadda Dr. Danjuma ke gudanar da siyasarsa ya bambanta da sauran ‘yan siyasa, don haka ya cancanci irin wannan yabo domin hakan zai ƙara masa ƙwarin guiwa.

Shuwaki ya ƙara da cewa duk da cewa a baya suna cikin jam’iyyu daban-daban, hakan bai hana su kyakkyawar mu’amala da mutunta juna ba.

A nasa ɓangaren, Kwamared Umar Sale Zara, wanda yana daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin samar wa matasa aiki da Dr. Danjuma ya bayar, ya bayyana PPS a matsayin “ɗaya tamkar dubu.”

Ya ce duk lokacin da Dr. Danjuma ya yi wani abu, baya neman a tallata shi ko a yi masa godiya, saboda gaskiya da riƙon amana da yake da su.

Ya ƙara da cewa mutane da dama sun amfana da kujerar da Dr. Danjuma yake kai, musamman ta fuskar ayyukan ci gaba da yake samarwa a yankuna daban-daban.

By ukarofi