Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wani mazaunin jihar Neja mai suna Victor Solomon ya bayyana alhini da kuka bayan da ya ce ya rasa ‘ya’yansa uku sakamakon harin jirgin saman soji da aka kai domin kai farmaki kan ‘yan bindiga a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa harin saman, wanda aka ce an kai shi kan maboyar ‘yan bindiga a yankin, ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula da dama ciki har da ‘ya’yan Solomon.
Majiyoyi da dama a jihar sun tabbatar wa manema labarai cewa sama da mutane goma ne suka rasa rayukansu sakamakon harin.
Victor Solomon mai shekaru 50, wanda mazaunin ƙauyen Guradnayi ne kusa da Kusasu a yankin Galadima-Kogo na ƙaramar hukumar Shiroro, ya ce har yanzu yana cikin matsanancin tashin hankali bayan faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa yana barci ne da misalin ƙarfe biyar na asubahin ranar Lahadi lokacin da harin ya afku, inda shi ma ya samu munanan raunuka a fuska.
Solomon ya ce ‘ya’yansa uku sun mutu tare da wasu mutane da dama.
“Ban san ko zan iya rayuwa bayan wannan ba. Na rasa ‘ya’yana uku sannan ni ma na samu munanan raunuka a fuskata. Ina cikin azaba sosai. Muna buƙatar taimakon gwamnati,” in ji shi cikin kuka.
Wani mazaunin yankin mai suna Gideon Bamaiyi ya shaida wa Arewa PUNCH cewa tun kafin harin jirgin saman, ‘yan bindigar sun bi ta yankinsu kamar yadda suka saba.
Ya ce mutane 13 ne suka mutu, ciki har da yara bakwai da suka fake a gidan babban yayansa lokacin harin.
Bamaiyi ya ƙara da cewa wasu mutum shida na karɓar magani a wani asibiti mai zaman kansa da ke garin Zumba a ƙaramar hukumar Shiroro.
Ya kuma bayyana cewa mutum biyar daga cikin waɗanda suka jikkata, ciki har da wata ƙaramar yarinya, har yanzu ba su farfaɗo ba.
Da yake mayar da martani kan lamarin, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Neja, Maurice Magaji, ya tabbatar da cewa sojoji sun kai hare-haren sama kan maboyar ‘yan bindiga a Shiroro.
Sai dai ya musanta cewa an kashe fararen hula, yana mai cewa ‘yan bindiga da masu ba su bayanai ne kawai aka kashe.
Ya ce kafin fara harin an gargadi jama’a su bar yankin, kuma duk wanda ya rage a wurin ana zargin yana taimaka wa ‘yan bindigar.
Shi ma hedikwatar tsaro ta ƙasa ta musanta kashe fararen hula a harin.
Daraktan yaɗa labarai na rundunar tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ya bayyana cewa harin ya biyo bayan bayanan sirri da suka nuna taruwar ‘yan bindiga a yankin Shiroro a ranar 9 ga Mayu, 2026.
A cewarsa, an kai hare-haren sama a ƙauyukan Katerma, Bokko, Kusasu da Kuduru, inda aka kashe kusan ‘yan bindiga 70 a Kusasu kaɗai.
Rundunar sojin ta jaddada cewa hare-haren sun yi daidai da wuraren da aka nufa kuma an gudanar da su bisa ingantattun bayanan sirri.
