Ficewar Obi da Kwankwaso ya sa jam’iyyarmu ta zauna lafiya – ADC

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa jam’iyyar ta samu zaman lafiya bayan ficewar manyan ‘yan siyasa ciki har da Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso.

Abdullahi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce duk da cewa ficewar jagororin biyu ta ba su mamaki, jam’iyyar ta wuce wannan mataki kuma tana ci gaba da kokarin gina hadakar jam’iyyun adawa domin kalubalantar gwamnatin APC.

Ya ce ADC na ganin cewa hadin kan jam’iyyun adawa ne kadai zai iya ba su damar kayar da jam’iyya mai mulki a zabukan 2027.

Abdullahi ya kuma amince cewa rashin haduwar manyan ‘yan adawa a karkashin inuwa daya babban koma baya ne ga yunkurin kafa kawance, amma ya jaddada cewa hakan ba zai hana ci gaba da gina gamayyar adawa mai karfi ba.

Ya bayyana fatan cewa har yanzu jam’iyyun adawa za su iya cimma matsaya kan tsayar da dan takara guda daya na shugaban kasa domin kalubalantar APC a 2027.

Game da batun tsarin karba-karba tsakanin yankuna, Abdullahi ya ce ADC za ta dauki matsaya ne bisa dabarun siyasa da za su ba ta damar samun rinjaye, ba wai kawai saboda daidaito na siyasa ba.

By ukarofi