Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Babban Daraktan Hukumar Kula da Jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC), Dakta Kayode Opeifa, ya nuna matuƙar damuwa kan yawaitar lalata kayayyakin layin dogo da kuma jifan jiragen ƙasa da duwatsu a hanyar Abuja zuwa Kaduna.
A cikin wani rubutu mai taken “Kare Layin Dogo, Kare Makomar Mu”, Dakta Opeifa ya bayyana cewa wasu ɓata-gari da ke fakewa a al’ummomin da ke kusa da layin dogo na kai hare-hare kan jiragen ƙasa yayin da suke tafiya, inda suke fasa tagogi tare da lalata gilashin gaba na wani jirgi da ke ɗauke da fasinjoji marasa laifi.
Ya bayyana waɗannan ayyuka a matsayin masu haɗari, rashin kishin ƙasa da kuma barazana ga rayukan jama’a, yana mai cewa hakan na kawo cikas ga manyan jarin da gwamnatin ƙasa ta saka wajen farfaɗo da harkar sufurin jiragen ƙasa.
Shugaban Hukumar NRC ya ce, layin dogo ba ƙarafa da tashoshi kawai ba ne, illa wata muhimmiyar hanya ce da ke haɗa al’umma, tana taimaka wa ma’aikata zuwa wuraren aiki, ‘yan kasuwa zuwa kasuwanni, ɗalibai zuwa makarantu da kuma iyalai zuwa wuraren ‘yan uwansu.
Ya ce abin takaici ne yadda gwamnati ke ci gaba da zuba kuɗaɗe wajen gyaran layukan dogo bayan shekaru masu yawa na sakaci, amma wasu marasa kishin ƙasa suka rungumi hanyar lalata kadarorin jama’a.
“Duk wani tagar jirgi da aka fasa, duk wani kayan layin dogo da aka lalata ko aka sace, kai hari ne kai tsaye kan ‘yan Nijeriya,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, talakawan ƙasa ne ke shan wahalar hakan ta hanyar tangarɗar ayyukan sufuri, ƙarin kuɗin gyara, jinkirin zirga-zirga da kuma hazarin rayukan fasinjoji.
Dakta Opeifa ya jaddada cewa babu wata ƙasa da za ta ci gaba idan har jama’arta na kallon muhimman kadarorin gwamnati tamkar marasa mai ita.
Ya ce ƙasashen da suka samu cigaba a harkar sufuri ba wai gwamnati kaɗai ta yi aiki ba, har ma jama’a sun ɗauki nauyin kare kadarorin ƙasa.
“Layin dogo mallakin kowa ne. Ba mallakin shugabannin NRC ko jami’an gwamnati kawai ba ne. Dukiyar ƙasa ce da aka gina da kuɗin jama’a domin amfanin jama’a,” ya bayyana.
Babban Daraktan ya yi kira ga matasa da sauran jama’a su guji lalata layin dogo, yana mai cewa saurayin da ke jifar jirgi da dutse na iya ɗaukar abin wasa ne, amma illarsa na iya jawo asarar rayuka da koma baya ga tattalin arzikin ƙasa.
Ya ce hanyar jirgin ƙasan Abuja–Kaduna ta zama muhimmiyar hanya ga dubban ‘yan Nijeriya saboda tana samar da ingantacciyar hanya mafi aminci, rahusa da sauƙi idan aka kwatanta da sufuri ta hanya.
Haka kuma ya bayyana cewa kama wasu da ake zargi da safarar kayan layin dogo da aka sace a hanyar Bauchi zuwa Kano alama ce da ke nuna yadda masu aikata wannan laifi ke ƙara haɗa kai a matsayin ƙungiyoyi.
Dakta Opeifa ya ce Hukumar NRC na aiki tare da jami’an tsaro, shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki domin ƙarfafa tsaro a layukan dogo, amma ya ce tsaro kaɗai ba zai wadatar ba face idan jama’a sun ɗauki matakin kare kadarorin ƙasa.
Ya buƙaci iyaye, shugabannin gargajiya, malamai da ƙungiyoyin matasa su riƙa wayar da kai tare da kai rahoton duk wani motsi mai kama da laifi a kusa da layukan dogo.
A cewarsa, kishin ƙasa ba wai magana kawai ba ce, domin wani lokacin kishin ƙasa na nufin kare kadarorin al’umma da hana lalacewar abubuwan da suka shafi cigaban ƙasa.
Ya ce farfaɗo da harkar jiragen ƙasa na ɗaya daga cikin manyan nasarorin gine-ginen more rayuwa da Nijeriya ta samu a ‘yan shekarun nan, don haka bai kamata a bari marasa kishin ƙasa su rusa nasarorin da ake samu ba.
