Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa tasirin gwamnatin tarayya ba zai iya sauya sakamakon zaɓen 2027 ba, yana mai cewa ‘yan Nijeriya za su fito su zaɓi shugabannin da suke so ba tare da tsoron tasirin siyasa ba.
Makinde ya bayyana hakan ne a yayin taron bunƙasa yawon buɗe ido na jihar Oyo da aka gudanar a cibiyar taruka ta jami’ar Ibadan, inda ya ce al’umma ba za su ci gaba da zama masu kallo kawai ba a siyasa.
Ya kuma ce gwamnatinsa ta kafa tsare-tsare masu ɗorewa da za su tabbatar da ci gaban jihar bayan wa’adinsa ya kare. A cewarsa, duk da zai iya ba da shawarar wanda zai gaje shi, mutanen Oyo ne za su yanke hukuncin wanda zai zama gwamna na gaba.
Gwamnan ya gargaɗi al’umma da su guji zaɓen wanda ba shi da ƙwarewar shugabanci, yana mai cewa kuskuren zaben shugaba na iya jefa jihar cikin matsala na tsawon shekaru huɗu.
A kan raɗe-raɗin cewa yana goyon bayan tsohon kwamishinan kuɗi, Bimbo Adekanbi, Makinde ya ce zai mara wa duk dan takarar da yake da kishin jihar Oyo tare da ƙwarewar shugabanci baya, ba tare da la’akari da jam’iyyarsa ba.
