Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON), ta samu amincewa da lasisin gudanar da ayyukan lafiya daga Ma’aikatar Lafiya ta Masarautar Saudiyya domin cibiyoyin lafiya da wuraren bayar da kulawar jinya da ta kafa domin kula da alhazan Nijeriya a lokacin aikin Hajjin shekarar 2026.
Rahoton ya bayyana cewa samun wannan lasisi ya bai wa tawagogin lafiya na hukumar damar fara gudanar da ayyukan kula da lafiya ga maniyyatan Nijeriya da ke ƙasar Saudiyya.
A matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen kiwon lafiyar alhazai, NAHCON ta tanadi asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya a wurare daban-daban domin samar da ayyukan lafiya na farko, ciki har da duba marasa lafiya, bayar da agajin gaggawa da kuma kula da ƙananan cututtuka ga maniyyatan Nijeriya.
Hukumar ta kuma bayyana cewa bisa ƙa’idojin aiki da aka shimfiɗa, duk wani alhaji da zai nemi kulawar lafiya a cibiyoyin NAHCON dole ne ya gabatar da katin Nusuk da fasfo ɗinsa na ƙasa da ƙasa domin tantancewa da rubuta bayanan jinyarsa.
NAHCON ta ƙara da cewa duk wani alhaji da ke buƙatar kulawa ta musamman ko kuma manyan ayyukan jinya za a tura shi zuwa asibitocin Saudiyya da aka tantance, ciki har da Asibitin King Fahd da sauran asibitocin da gwamnati ta ware domin kula da alhazai.
Hakazalika, hukumar ta tabbatar da cewa asibitinta da ke birnin Madina ya kwashe kwanaki huɗu yana gudanar da aiki yadda ya kamata, inda yake ba da kulawar lafiya da taimakon jinya ga alhazan Nijeriya da ke cikin birnin.
Daga cikin asibitocin da suka samu lasisin gudanar da aiki akwai cibiyar lafiya ta NAHCON da ke yankin Shara Sittin a Makkah, wadda take a otel ɗin Humaira da ke titin Ummul-ƙura kusa da tsohon gidan man Al-Maatani.
Haka kuma akwai cibiyar lafiya ta Misfalah da ke yankin Al-Tadwa a Makkah, wadda take a otel ɗin Maatouƙ Al ƙarhi bayan Millennium Hotel da ke titin Ibrahim Khalil.
Sannan akwai cibiyar lafiya ta yankin Mansour Street da ke cikin gidan Niger House No.1 bayan Muasasat Alnaƙd a birnin Makkah.
Hukumar ta bayyana cewa samun wannan lasisi wani babban ci gaba ne a shirye-shiryen Hajjin 2026, tare da nuna jajircewarta wajen kare lafiya, tsaro da jin daɗin alhazan Nijeriya gaba ɗaya a lokacin zamansu a Masarautar Saudiyya.
