Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsohon Shugaban ƙasar Nijeriya, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), ya bayyana cewa sabon littafin tarihin rayuwarsa da ya fitar an rubuta shi ne domin fayyace manufofi da matakan da gwamnatinsa ta ɗauka a lokacin Yaƙin Basasar Nijeriya, ba domin tayar da tsoffin raɗaɗin yaƙin ba.
Rahoton da aka wallafa ya nuna cewa Gowon ya bayyana hakan ne gabanin ƙaddamar da littafin nasa mai shafuka 881, wanda za a yi a ranar 19 ga watan Mayun 2026 a Cibiyar Taro ta ƙasa da Aasa ta Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja.
A cewar sanarwar da kamfanin Havilah Group, masu wallafa littafin, suka fitar a ranar Talata, ana sa ran manyan shugabannin siyasa, tsoffin hafsoshin soja, jami’an diflomasiyya da manyan jami’an gwamnati za su halarci taron, yayin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kasance babban baƙo na musamman.
Haka kuma, tsohon Ministan Tsaro kuma tsohon Babban Hafsan Sojin ƙasa, Janar Theophilus Danjuma (mai ritaya), ne zai jagoranci ƙaddamar da littafin.
Da yake bayani kan dalilin rubuta tarihin, Gowon ya ce ya ga wajibi ya fito da nasa bayanin ne saboda shekaru da dama ana rubuce-rubuce kan lokacin yaƙin daga mahangogi daban-daban, ba tare da cikakken bayyana tunaninsa da dalilan da suka jagoranci matakan da ya ɗauka a matsayin shugaban ƙasa ba.
“Lokacin da na yanke shawarar rubutawa, manufata ba wai sake buɗe tsoffin raunuka ba ce, illa dai fayyace yadda na kalli manufofi da tsare-tsaren gwamnati a wani lokaci da wasu suka daɗe suna ba da labarinsa ta hanyarsu,” inji Gowon.
Ya ƙara da cewa, rayuwarsa labari ne na ƙudurci da yanayi suka gwada a lokacin da ƙasa ke cikin tsaka mai wuya tsakanin fata da haƙiƙani.
Ana sa ran littafin zai ƙunshi bayanansa kan muhimman abubuwan da suka faru bayan samun ’yancin kai, musamman Yaƙin Basasar Nijeriya da aka gwabza daga shekarar 1967 zuwa 1970.
Yaƙin, wanda ya biyo bayan yunƙurin yankin Gabas na kafa Jamhuriyar Biyafara, na daga cikin mafi muhimmanci kuma mafi tayar da hankali a tarihin Nijeriya, inda miliyoyin mutane suka rasa matsugunansu tare da asarar rayuka masu yawa.
Janar Gowon, wanda ya hau mulki a ranar 1 ga watan Agustan 1966 yana da shekara 31 kacal, shi ne ya jagoranci ƙasar a lokacin yaƙin kafin daga bisani ya ɓullo da manufar “Ba Mai Nasara, Ba Wanda Aka Ci Galaba,” wadda aka ƙirƙira domin sulhu, sake haɗa kan al’umma da dawo da zaman lafiya bayan yaƙin.
Rahoton ya ce tsohon shugaban mulkin sojan zai kuma yi bayani kan rayuwarsa ta farko, aikinsa na soja da yadda ya samu kansa a karagar mulki bayan rikice-rikicen siyasa da juyin mulkin shekarar 1966.
An haifi Gowon a shekarar 1934 a yankin da yanzu ake kira Jihar Filato. Ya kasance ɗaya daga cikin shugabannin Nijeriya mafi ƙanƙantar shekaru, inda ya shafe shekaru tara yana mulki kafin a hamɓarar da shi a juyin mulkin soja ba tare da zubar da jini ba a watan Yulin 1975 yayin da yake halartar taron ƙungiyar Haɗin Kan Afirka ta OAU a Uganda.
Bayan saukarsa daga mulki, Gowon ya ci gaba da gina suna a matsayin dattijon ƙasa mai fafutukar samar da zaman lafiya, haɗin kan addinai da ayyukan jinƙai.
A shekarar 1984 ya samu digirin digirgir a fannin Kimiyyar Siyasa daga Jami’ar Warwick, sannan daga baya ya kafa cibiyar Yakubu Gowon Centre domin inganta zaman lafiya, shugabanci nagari da ci gaban ƙasa.
