CBN ya tilasta bankuna wallafa asusun da aka yi shekaru 10 ba a yi hulɗa da su ba

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wasu manyan bankunan Nijeriya huɗu sun wallafa bayanan asusun ajiyar kuɗi 321,181 da suka daɗe ba tare da an yi hulɗa da su ba, domin bin umarnin da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayar, lamarin da ya jawo muhawara kan yadda ake sanar da kwastomomi, kare sirrin bayanai da kuma sake ɗaga irin waɗannan asusu.

Bankunan da suka fitar da jerin sun haɗa da Access, Union, Stanbic IBTC da Fidelity, bayan sabon tsarin da CBN ya fitar a watan Yulin 2024 wanda ya umarci bankuna su wallafa bayanan asusun da suka yi sama da shekara 10 ba tare da motsi ba, watanni shida kafin a mayar da kuɗaɗen cikin Asusun Ajiyar Kuɗaɗen Da Ba A Karɓa Ba na CBN.

Rahoton ya nuna cewa asusun da aka wallafa sun haɗa da na mutane ɗaiɗaiku, kamfanoni, ƙungiyoyin haɗin gwiwa, coci-coci, ƙungiyoyi da ƙananan sana’o’i.

Bankin Access ne ya fi yawan asusun da aka wallafa, inda ta fitar da bayanan asusu 243,934, ciki har da na mutane 122,390 da kuma na kamfanoni 120,718.

Ita ma Fidelity Bank ya wallafa asusu 61,900, inda kusan kashi 79 cikin 100 na su na kamfanoni ne. Stanbic IBTC kuwa ta fitar da asusu 26,135 yayin da Union Bank ta wallafa guda 212.

Bayanan sun nuna cewa akwai yawaitar asusun da suka daina aiki a tsakanin ƙananan da matsakaitan sana’o’i, kamfanonin mai da iskar gas, masu harkar sufuri, makarantu, coci-coci da kamfanonin kasuwanci, musamman a yankunan kasuwanci na Legas, cibiyoyin harkar mai na Fatakwal da manyan cibiyoyin kasuwanci a Arewacin Nijeriya.

Sai dai wasu bankunan sun bi wata hanya ta daban. Bankin UBA ya wallafa jerin ribar hannun jari da ba a karɓa ba maimakon asusun da suka daina aiki. First Bank da Zenith Bank kuwa sun samar da shafukan bincike domin kwastomomi su duba ko sunansu na cikin jerin, yayin da GTBank ta fitar da ƙa’idojin sake kunna asusu ba tare da wallafa sunaye ba. Ecobank ma ya samar da hanyoyin sake tada asusu amma bai fitar da bayanan asusun ba.

Masana tattalin arziki da shugabannin harkokin kasuwanci sun bayyana cewa wannan mataki ya fito da giɓin da ke akwai wajen sadarwar bankuna da kwastomominsu, tare da tayar da tambayoyi kan sirrin bayanai.

Daraktan Cibiyar Bunƙasa Kamfanoni Masu Zaman Kansu, Muda Yusuf, ya ce wannan mataki na nuna cewa bankuna ba sa yin isasshiyar hulɗa da kwastomominsu.

Ya ce, “Ina ganin wannan yana nuna buƙatar bankuna su ƙara sadarwa da kwastomominsu.” Ya kuma danganta yawaitar asusun da suka mutu da rufe kamfanoni da kuma wahalar sake kunna asusun.

Shi ma Farfesa Akpan Ekpo na Jami’ar Uyo ya nuna damuwa kan wallafa bayanan a bainar jama’a, yana mai cewa hakan na iya tauye sirrin mutane.

Tsohon shugaban ƙungiyar Kasuwanci da Masana’antu ta Legas (LCCI), Gabriel Idahosa, ya bayyana cewa haɗewar bankuna, sauya wurin zama, rasuwa da kuma rugujewar kasuwanci na daga cikin abubuwan da ke haddasa daina amfani da asusu.

Ya kuma yi gargaɗin cewa wallafa sunaye na iya jawo rikice-rikicen iyali da kuma ƙalubalen shari’a dangane da sirrin bayanai.

A ƙarƙashin sabon tsarin, CBN ya bayyana cewa kuɗaɗen da suka daɗe ba tare da an yi hulɗa da su ba na iya faɗawa cikin zamba da amfani ba bisa ƙa’ida ba.

By ukarofi