Matuƙan jirgi sun yi gargaɗi kan ƙarancin mai a Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar Matuƙan Jiragen Sama da Injiniyoyi ta ƙasa (NAAPE), ta yi gargaɗin cewa ƙarancin man jiragen sama da aka fi sani da Jet A1 na barazana ga tsaron zirga-zirgar jirage, ɗorewar kamfanonin sufurin jiragen sama da kuma zaman lafiyar ma’aikata a harkar sufurin jiragen sama a Nijeriya.

A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Kyaftin Bunmi Gindeh, ya fitar a Abuja ranar Lahadi, ya bayyana lamarin a matsayin matsala mai matuƙar muhimmanci da ke buƙatar gaggawar shiga tsakani daga gwamnatin tarayya.

Gindeh ya yi gargaɗin cewa gajiyawar da ma’aikatan jirage ke fuskanta sakamakon jinkiri da tangarɗar zirga-zirgar jirage na iya rage matakan kariya da tsaro a harkar sufurin jiragen sama.

Ya buƙaci Gwamnatin Tarayya, da NCAA, da NMDPRA, tare da masu samar da man jiragen sama, su ɗauki matsalar ƙarancin Jet A1 a matsayin batu na gaggawa da ya shafi tsaron ƙasa baki ɗaya.

A cewarsa, “Yawan tangarɗar jadawalin tashi da saukar jirage da ƙarancin man Jet A1 ya haifar ya sa lokutan aikin ma’aikatan jirage suka zarce yadda aka tsara. Gajiya na rage ƙwaƙwalwa da saurin fahimta, sannan mafi haɗari shi ne tana rage saurin tantance yanayin da ake ciki yayin tafiyar jirgi.”

Ya ƙara da cewa, a fannin sufurin jiragen sama na duniya, kula da gajiyar matuƙa da sauran ma’aikatan fasaha na daga cikin manyan abubuwan da hukumomi da kamfanoni ke bai wa muhimmanci, inda ake saka ƙa’idoji masu tsauri kan tsawon lokacin aiki domin kare lafiyar fasinjoji da jiragen sama.

Shugaban ƙungiyar ya bayyana cewa tsawaita lokutan aiki na iya lalata ingancin yanke shawara, sadarwa da kuma yadda ake tunkarar matsalolin gaggawa yayin tafiyar jirgi.

NAAPE ta kuma yi gargaɗin cewa matsalar ta fara yin tasiri ga harkokin kasuwancin kamfanonin jiragen sama da kuma jin daɗin ma’aikata, lamarin da ka iya ƙara jefa masana’antar cikin matsin tattalin arziki idan ba a shawo kan matsalar cikin gaggawa ba.

By ukarofi