‘Yan sanda sun kama wanda ake zargi bayan ceto jaririn kwana 10 a Zamfara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Juma’a Rundunar ‘Yan sanda a Jihar Zamfara ta yi nasarar daƙile wani yunƙurin safarar ɗan-adam da kuma satar wani jaririn kwana 10 daga Babban Asibitin Kauran Namoda.

An cimma haka ne a lokacin da aka kai ƙara ofishin hukumar a Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda akan sace jaririn.

A wata sanarwa da Kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar ya fitar a yau Asabar, ya ce a yayin bincike, an gayyaci ma’aikatan asibitin da ke bakin aiki a lokacin da abin ya faru domin taimaka wa binciken.

Bayan haka, a jiya da misalin ƙarfe 8:35 na safe aka yi nasarar gano jaririn a wani ƙauye da ke kusa da inda aka yi awon-gaba da shi.

Jami’in hulɗa da jama’ar ya bayyana cewa an samu yaron cikin aminci tare da damƙa shi ga iyayensa na asali.

Haka kuma, an kama wani matashi ɗan shekara 27 bisa tuhumar sa da hannu a laifin, wanda a yanzu haka yana hannu.

Akan haka ne Kwamishinan ‘yan sandan Zamfara, Ahmad Bello ya jinjina wa al’ummar yankin bisa gudunmawar da suka bayar wajen cimma nasarar gano jaririn, yana mai jaddada musu ƙoƙarin jami’ansu na kawo ƙarshen kowane irin ta’addanci da ya addabe su a sassan jihar.

By Babaji