Daga JOHN D. WADA a Lafia
Wani sashe na wani babban sakatariyar gwamnatin tarayya da ake kira Muhammad Sidi Bage Federal Secretariat dake Lafia babban birnin Jihar Nasarawa ya kama da wuta da yammacin jiya Asabar inda lamarin ya jefa ma’aikata da mazauna kusa da sakatariyar cikin fargaba.
A cewar ganau da abin ya auku a idonsu sun bayyana wa wakilinmu a jihar cewa wutar ta tashi ne daga wani ofis dake bene na biyu na ginin sakatariyar mai hawa uku inda hayaƙi mai yawa da kauri ya fara fita daga yankin da abin ya faru ya kuma mamaye sauran ofishoshin baki ɗaya lamarin da ya haifar da tashin hankali tsakanin ma’aikata da baƙi da mazauna yankin da sauransu.
Koda yake shaidu na gani da idon sun ce matakai cikin sauri da gaggawa da wasu jami’an hukumar kashe gobara na tarayya tare da haɗin gwiwar takororinsu na jihar suka yi sun samu nasarar kashe wutar a ƙarshe kuma suka hana ta yaɗuwa zuwa sauran sassan sakatariyar.
Har ila yau wakilin namu ya kuma ruwaito cewa har zuwa lokacin da ake haɗa wannan rahoto ba a iya gano ainihin musabbabin aukuwar gobarar daga wannan sashin babban sakatariyar ba, amma jami’an kashe gobarar na cigaba da gudanar da cikakken bincike akan hakan.
