
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Zakaran ɗan ƙwallon duniya, Cristiano Ronaldo ya ƙi karɓar shaidarsa ta samun matsayi na biyu bayan Al-Nassr ta sha kaye a hannun ƙungiyar Gamba Osaka ta ƙasar Japan da ci 1 da 0 a wasan ƙarshe na Kofin Zakarun Asiya a yammacin ranar Asabar.
An ga yadda ɗan wasan ya fice daga filin wasan a lokacin da alƙalin wasa ya busa ƙararrawar kammala wasan.
Rahotanni sun bayyana cewa, ɗan wasan gaban bai je wajen kociyan ƙungiyarsa ba tare da sauran ‘yan wasa a lokacin da suka je amsar kyautar tagulla.
A minti na 29 ne ɗan wasan Gamba Osaka na ƙasar Turkiyya Deniz Hummet ya samu damar zura ƙwallo ɗaya tilo da ta ba su nasara akan su Ronaldo.
Wannan rashin nasara ya sanya Ronaldo cikin halin cigaba da jiran samun damar lashe babban kofi tun bayan zuwansa ƙungiyar ƙasar Saudiyyar a ƙarshen 2022.
A yanzu dai, Al-Nassr ka iya lashe kofin gasar League Championship matuƙar ta doke Damac da ke fafutukar faɗawa ƙaramin rukuni a ranar Alhamis.
