An harbe mutum ɗaya yayin da rikici ya ɓarke a wajen taron zaɓen fidda gwanin APC a Filato

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An shiga firgici a ranar Lahadi yayin taron jam’iyyar APC na zaɓen fidda gwani na ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai a Ƙaramar Hukumar Mangu da ke Jihar Filato bayan harbe wani mazauni a wajen taron.

An harbe Sani Abdullahi, wanda dan ƙauyen Kasuwan Ali ne a lokacin da aka yi gaba da gaba tsakanin jami’an tsaro da matasa masu zanga-zanga.

Wani shaida ya ce al’amarin auku ne bayan fusata akan jinkirin fara zaɓen fidda gwanin da aka shirya farawa da safe, wanda ba a cimma haka ba saboda rashin ganin malaman zaɓe.

Wani mazaunin yankin mai suna, Ibrahim Sale, ya ce jinkirin da kaa samu ne ya haifar da fushi acikin mambobin jam’iyya da magoya baya, waɗanda suka zargi masu shirya taron da ƙoƙarin haddasa tsaiko a harkokin zaɓen da gangan.

A cewarsa, al’amarin ya yi ƙamari ne a lokacin da wasu matasa suka tare hanyar fita, inda suka tirje akan babu jami’in zaɓe da zai fita sai an gudanar da zaɓen.

A lokacin ne jami’an tsaro suka yi ƙoƙarin shiga tsakani tare da yunƙurin tarwatsa mutanen da suka yi cincirindo a wajen.

Daga bisani matasan sun fara jifar jami’an tsaron da duwatsu, lamarin da ya sa suka mayar da martani da harbe-harben bindigu, idna a ciki aka samu alburushin da ya yi ajalin Abdullahi.

By Babaji