Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ƙungiyar Grassroots Mobilisation for Tinubu-Dikko 2027 ta ƙaddamar da shuwagabannin ƙungiyar tare da basu takardar kama aiki domin bada gudunmuwa wajen tazarcen Tinubu-Dikko a zaɓen.
Ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin Hon. Abubakar Tsanni Soja ta rantsar da mambobin ta a ofishin ta dake Kanbarawa a cikin birnin Katsina.
Dr. Abubakar Soja Tsanni, wanda shi ne kodinetan ƙungiyar GMTD, ya ce an kafa ƙungiyar ne domin wayar da kan jama’a, haɗa matasa da mata, da kuma tallafa wa shirye-shiryen ci gaba da gwamnatin tarayya da ta jihar Katsina.
Da yake jawabi ministan gidaje da tsara birane Injiniya Dr. Muttaqa Rabe Darma ya gabatar da jawabin inda yayi kira ga matasa da su fito domin ƙara marawa Tinubu da Raɗɗa baya domin zarcewa mulki karo na biyu.
Ya kuma ce ƙungiyar GMTD za ta bayar da jari ga mutane kusan 700 nan gaba domin tallafa wa matasa da jari don dogaro da kai.
An rufe taron da addu’oin neman zaman lafiya ga jihar Katsina da Najeriya baki ɗaya.
Kwamishinan albarkatun ruwa da shugaban ƙaramar hukumar Katsina Ishaq Miqidad Saude na daga cikin waɗanda suka halarci bikin.
