
Tsohon Ministan Tsaro, Theophilus Ɗanjuma, ya bada gudunmawar Naira biliyan 3 a yayin ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Yakubu Gowon a Abuja ranar Talata.
Haka kuma attajirin Afrika kuma shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 500 domin tallafawa ƙaddamar da littafin.
Littafin mai suna “My Life of Duty and Allegiance”, wanda ke ɗauke da babi 20, ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, jami’an diflomasiyya da manyan hafsoshin soja. Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ne ya wakilci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a wajen taron.
An bayyana cewa Danjuma, wanda tsohon babban hafsan tsaro Janar Martin Luther Agwai ya wakilta, ya kuma bayar da umarnin sayen kwafe 12 na littafin domin rabawa ɗakunan karatu na jami’o’i 20 da suka taɓa bai wa Gowon digirin girmamawa.
A jawabin yabo da ya gabatar, Danjuma ya bayyana Gowon a matsayin babban dattijon ƙasa mai rai, jagora na duniya da kuma mutumin da jagorancinsa ya taimaka wajen hana tarwatsewar Najeriya a lokacin yaƙin basasa.
Shi ma wakilin Dangote, Mansur Ahmed, ya ce shugaban nasa ya sayi kwafe 25 na littafin kan Naira miliyan 500 domin karrama Gowon, yana mai cewa zaman lafiyar da Gowon ya samar ya ba Dangote damar girma har ya gina daular kasuwanci a Afrika.
Sauran fitattun mutane da kamfanoni ma sun sayi kwafen littafin, ciki har da shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdul Samad Rabiu, wanda ya sayi littattafai kan Naira miliyan 25.
