Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin jihar Anambra ƙarƙashin jagorancin Gwamna Chukwuma Soludo ta sanar da sabbin dokoki masu tsauri domin rage yawaitar kashe kuɗaɗe wajen jana’iza da kuma sauƙaƙa wa iyalan mamata nauyin da ake ɗora musu yayin zaman makoki.
Sabuwar dokar, wacce Majalisar Dokokin Jihar Anambra ta amince da ita, ta tanadi ƙa’idoji domin tsara yadda ake gudanar da jana’iza da bukukuwan binne mamata a faɗin jihar.
A cewar gwamnatin jihar, an kafa dokar ne domin daƙile al’adun gudanar da jana’iza cikin almubazzaranci, waɗanda suka daɗe suna jefa iyalan mamata cikin matsin tattalin arziki.
Haka kuma, gwamnati ta bayyana cewa dokar na da nufin ƙara bunƙasa ayyukan tattalin arziki ta hanyar hana tsawaita bukukuwan jana’iza da ke hana mutane gudanar da ayyukansu a ranakun aiki.
Sabuwar dokar ta haramta gudanar da jana’iza daga Litinin zuwa Juma’a, inda ta ƙayyade cewa duk jana’iza za a riƙa yi ne a ranar Asabar kawai. Dokar ta kuma tanadi cewa dole ne a kammala duk wani bikin jana’iza cikin rana guda kacal.
Kazalika, an hana bayar da manyan kyaututtuka ga iyalan mamaci yayin ta’aziyya. A ƙarƙashin dokar, mutum ba zai ba iyalan mamaci kyautar da ta wuce kuɗi, tulun giyar dabino guda ɗaya, kwali ɗaya na giya ko kuma kiret ɗaya na lemo ba. Haka kuma gwamnati ta haramta kai shanu, awaki, buhunan shinkafa da sauran tsadaddun kayayyaki wajen jana’iza ko zaman ta’aziyya.
Dokar ta soke zaman makoki na dare gaba ɗaya, yayin da ta ƙayyade cewa duk addu’o’i, wa’azi ko hidimomin addini dole ne su ƙare kafin ƙarfe 9 na dare. An kuma hana bayar da abinci, abubuwan sha, kaɗe-kaɗe ko nishaɗi a irin waɗannan taruka.
Baya ga haka, gwamnati ta hana liƙa hotunan mamata a allunan talla ko ina cikin jihar, sai dai alamomin nuna hanya zuwa wajen jana’iza, waɗanda dole ne kada a kafa su kafin kwanaki bakwai zuwa ranar jana’iza. Sabuwar dokar ta kuma haramta rawa da akwatin gawa tare da hana nuna akwatunan gawa domin talla ko sayarwa a bainar jama’a. An ƙayyade cewa masu aikin jana’iza ba za su wuce mutum shida ba yayin gudanar da ayyukansu.
Haka kuma, an tanadi cewa gawar mamaci ba za ta wuce watanni biyu a ɗakin ajiye gawa ba. Duk gawar da ta zarce wannan lokaci za a iya ayyana ta a matsayin “gawar da aka ƙi karɓa”, sannan gwamnati ta binne ta a maƙabartar da ta ware. Dokar ta kuma hana gudanar da jana’iza ta biyu sai a wasu lokuta da suka shafi al’ada ko gado. An taƙaita sanya kayan haɗin kai da aka fi sani da “aso ebi” ga iyalai na kusa, ƙungiyoyin coci, ‘yan uwa da wasu ƙungiyoyi na gargajiya kawai.
Domin tabbatar da bin dokar, gwamnatin jihar ta ce za ta kafa kwamitocin sa ido a matakin al’umma domin kula da rajistar mace-mace, amincewa da jana’iza da kuma tabbatar da ana bin dokar yadda ya kamata.
Haka kuma, gwamnati ta haramta wasu al’adun matasa da take ganin suna tayar da hankali yayin jana’iza, ciki har da nuna hotunan mamaci a bainar jama’a, lalata amfanin gona ko dukiyoyin jama’a, da kuma amfani da bindiga ba bisa ƙa’ida ba. Dokar ta yi gargaɗin cewa duk wanda ya karya waɗannan ƙa’idoji zai fuskanci tarar Naira dubu 100 ko ɗaurin watanni shida a gidan yari, ko kuma duka biyun tare. Gwamnatin jihar ta ce matakin na da nufin dawo da tsari a harkokin jana’iza tare da rage wa iyalai nauyin kashe kuɗaɗe masu yawa.
