Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Sabbin takardun shari’a da aka fitar sun nuna cewa, Kabiru Umar, wanda aka fi sani da Kabiru Sokoto, wanda kuma aka samu da laifi kan harin bom na ranar Kirsimeti ta shekarar 2011 da aka danganta da ƙungiyar Boko Haram, ya samu digiri a fannin ilimin halattu, wato Biology, yayin da yake zaman hukuncin ɗauri.
Lauyoyinsa ne suka bayyana hakan a cikin wata sanarwa da suka fitar yayin da suke sanar da ɗaukaka ƙarar hukuncin da aka yanke masa a shekarar 2013.
A cewar tawagar lauyoyin, Kabiru Sokoto ya ci gaba da mayar da hankali kan gyaran rayuwarsa da neman ilimi duk da yanayin da yake ciki a gidan yari, inda suka ce ya kammala karatu a National Open Uniɓersity of Nigeria tare da samun digiri a fannin ilimin halittu (Biology).
Sanarwar, wacce kamfanin lauyoyi na Don Akaegbu & Company mai hedikwata a Legas ya sanya wa hannu a ranar 14 ga Mayu, ta bayyana wannan nasara a matsayin wata alama ta ƙoƙarinsa wajen inganta rayuwarsa duk da ƙalubalen da yake fuskanta.
An samu Kabiru Sokoto da laifi ne a ranar 20 ga Disamba, 2013 a gaban Babbbar Kotun Tarayya da ke Abuja, bayan shari’ar da ta shafi harin bom da aka kai cocin St. Theresa Catholic Church da ke Madalla a Jihar Niger a ranar Kirsimeti ta shekarar 2011.
Harin ya yi sanadiyyar mutuwar kusan masu ibada 35 tare da jikkata wasu da dama, lamarin da ya girgiza ƙasar a lokacin.
Sai dai lauyoyinsa sun ce tuhume-tuhumen da aka gabatar a kansa ba su zarge shi kai tsaye da aikata harin ko jagorantar harin bom ɗin ba. A cewarsu, abin da ake tuhumarsa da shi shi ne zargin cewa yana da masaniya game da harin tun kafin afkuwarsa amma bai sanar da hukumomin tsaro ba.
Lauyoyin sun bayyana cewa bambancin da ke tsakanin zargin hannu kai tsaye a harin da kuma zargin sanin shirin tun da wuri na daga cikin manyan batutuwan da suke son kotun ɗaukaka ƙara ta sake dubawa.
Takardun ɗaukaka ƙarar sun kuma nuna cewa tawagar lauyoyin na ƙalubalantar sahihanci da karɓuwar hujjojin da aka yi amfani da su wajen yanke masa hukunci.
Sun ce an samu tsaiko wajen gabatar da ɗaukaka ƙarar saboda wasu matsaloli da suka haɗa da mutuwar lauyoyinsa guda biyu da suka gabata, yawaitar canja masa wurin tsarewa daga gidan yari zuwa wani, da kuma matsin tattalin arziki da iyalansa suka fuskanta.
Haka kuma, sun nuna damuwa kan ko kotun farko ta yi cikakken nazari kan bayanan kariyar da aka gabatar a lokacin shari’ar.
Lauyoyin sun buƙaci jama’a da su bari tsarin shari’a ya ci gaba cikin lumana, suna mai jaddada cewa ya kamata a tantance alhakin aikata laifi ne bisa hujjojin da aka gabatar a kotu, ba wai bisa ra’ayin jama’a ko matsin lamba daga waje ba.
