Yadda NJC ta hukunta alƙalai da dama kan rashin bin dokokin shari’a

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Majalisar Kula da Harkokin Shari’a ta ƙasa (NJC) ta dakatar da wasu alƙalai biyu daga aiki na tsawon shekara guda ba tare da albashi ba bisa zargin rashin ɗa’a da karya ƙa’idojin aiki.

Majalisar ta kuma amince da tura sunayen wasu alƙalai 12 domin naɗa su a matsayin alƙalan Kotun ɗaukaka ƙara ta Nijeriya.

An cimma waɗannan matsayai ne yayin taron majalisar karo na 111 wanda Babbar Alƙalin Nijeriya, Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta jagoranta.

Haka zalika, NJC ta yi watsi da ƙorafe-ƙorafen wasu alƙalai takwas daga ɓangaren shari’ar jihar Imo da aka yi wa ritaya dole bisa zargin sauya shekarunsu na haihuwa.

Alƙalan da aka ba da shawarar ɗaga matsayinsu zuwa Kotun ɗaukaka ƙara sun haɗa da Yakubu Abdulhammeed Mohammed, Abodunde Monisola Oluwatoyin, Ajuwa Raphael, Abua Elias Ojie, Ijohor Mbalamen Jennifer, Shuaibu Sabiu Bala, Omotosho James Kolawole, Nwite Emeka, Buba Dauda Njane, Kado Sanusi, Ademola Enikuomehin da kuma Dadom Julcit ɓeronica.

Majalisar ta dakatar da Mai Shari’a Ibrahim D. Shekarau na Babbar Kotun Jihar Nasarawa kan zargin rashin bin ƙa’idojin aiki bayan ya bayar da umarnin gaggawa da ya sa aka cire naira miliyan bakwai daga asusun bankin wani mai ƙara.

A cewar NJC, alƙalin bai bi tanadin doka ba tare da nuna rashin gaskiya wajen gudanar da shari’ar.

Haka kuma, an dakatar da Mai Shari’a Edward A.E. Okpe na Babbar Kotun Tarayya da ke Babban Birnin Tarayya Abuja saboda karya haƙƙin sauraron ɓangarorin da abin ya shafa a wata shari’ar rikicin aure.

Majalisar ta bayyana cewa alƙalin ya bayar da umarnin gaggawa wanda ya kai ga soma matakin hukunci kan wani mutum ba tare da ba shi damar kare kansa ba.

A wani mataki kuma, NJC ta tsawaita wa’adin riƙon kwarya na Mai Shari’a Ijeoma Agugua a matsayin Babbar Alƙalin Jihar Imo na tsawon watanni uku har sai an naɗa cikakkiyar babbar alƙali.

Alƙalan jihar Imo da aka yi wa ritaya kuma aka yi watsi da ƙorafinsu sun haɗa da B.C. Iheka, K.A. Leaweanya, Okereke Chinyere Ngozi, Innocent Chidi Ibeawuchi, Ofoha Uchenna, Eɓeryman Eleanya, Rosemond Ibe da T.N. Nzeukwu.

Sai dai majalisar ta mayar da Mai Shari’a T.I. Nze bakin aikinsa a Kotun ɗaukaka ƙara ta Gargajiya ta Jihar Imo bayan nazarin wasu sababbin hujjoji da ya gabatar.

NJC ta kuma bayyana cewa ta duba ƙorafe-ƙorafe guda 98 da aka shigar kan jami’an shari’a, inda ta yi watsi da guda 68 saboda rashin hujja, ta gargadi alƙalai huɗu, sannan ta bayar da umarnin ci gaba da bincike kan ƙorafe-ƙorafe guda 11.

Bugu da ƙari, majalisar ta amince da aika wasiƙun neman bayani guda 256 ga jami’an shari’a bisa matsalolin da suka shafi ƙwarewa da gudanar da aiki.

By ukarofi