Gwamnatin Legas ta gargaɗi jama’a kan cin ruɓaɓɓen tumatir

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kare Haƙƙin Masu Amfani da Kaya ta Jihar Legas ta yi gargaɗi ga mazauna jihar da su guji cin tumatir da suka lalace ko waɗanda suka ruɓe, tana mai cewa hakan na haifar da barazana ga lafiya.

An fitar da wannan gargaɗi ne a ranar Lahadi cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta wallafa a shafinta na ɗ, inda hukumar ta buƙaci jama’a su ƙara yin taka-tsantsan wajen sayen kayan abinci.

Babban Manajan Hukumar Kare Haƙƙin Masu Amfani da Kaya ta Jihar Legas, Afolabi Solebo, ya yi kashedi kan saye ko amfani da tumatir da ke nuna alamun ruɓewa masu launin fari, kore ko baƙi.

Ya bayyana cewa, akwai wabi cuta ta fungi da ke fitowa a jikin ruɓaɓɓun tumatir, wanda ka iya samar da guba irin ta aflatoɗins, wadda ka iya haddasa matsalolin lafiya masu tsanani ciki har da lalacewar hanta da sauran cututtuka.

“Ana tantance lafiyar mutum ne ta irin abin da yake ci lokaci zuwa lokaci,” inji shi, yayin da yake jaddada muhimmancin amfani da abinci mai tsafta da inganci.

Solebo ya kuma yi gargaɗin cewa dafa tumatir ta hanyar tafasawa ko soyawa ba ya kashe irin wannan guba, yana mai cewa duk tumatir da suka gurɓace ba su da lafiya ko da an sarrafa su.

Ya shawarci jama’a kada su ruɗu da arha ko rahusar kayan da suka lalace, yana mai jaddada cewa lafiya ta fi muhimmanci fiye da rage kuɗi.

Hukumar ta kuma buƙaci masu saye su riƙa duba kayan abinci da kyau kafin saya, su guji duk kayan da suka nuna alamun lalacewa tare da zubar da marasa lafiya yadda ya kamata.

Solebo ya ƙara da kira ga jama’a da su riƙa kai rahoton ’yan kasuwar da ke sayar da abinci marar lafiya ko wanda wa’adinsa ya ƙare.

A cewarsa, hukumomin sa ido sun bazu a kasuwanni domin daƙile sayar da gurɓatattun kayayyaki.

Gargaɗin na zuwa ne bayan wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, wanda ya nuna wasu mata biyu suna kai tumatir da barkono masu tsutsotsi zuwa injin niƙa a yankin Mile 12 domin sarrafa su don abinci.

Mahukunta sun tabbatar da cafke mutum guda dangane da lamarin, yayin da ake ci gaba da neman wata da ake zargi da hannu a cikin abin da ya faru.

By ukarofi