Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Yayin da birane da dama a duniya ke kashe maƙudan kuɗaɗe wajen gyaran ramukan hanyoyi da kuma fama da tarin robobi da ke zama shara, ƙasar Netherlands ta ɓullo da wata sabuwar dabara ta gina titin kekuna mai amfani da robobi da aka sake sarrafawa.
Titin, wanda aka ƙaddamar a ƙaramar hukumar Zwolle tun ranar 11 ga Satumban 2018, yana da tsawon mita 30 kuma an yi shi da robobin da suka kai daidai da kofunan roba sama da 218,000 da aka sake sarrafawa.
Kamfanin Waɓin, ɗaya daga cikin abokan haɗin gwiwar aikin PlasticRoad, ne ya bayyana hakan. Aikin ya samu haɗin gwiwar kamfanonin KWS, Wavin da kuma Total.
Sabon tsarin ya dauki hankalin jama’a ne ba wai saboda maye gurbin kwalta da roba kawai ba, har ma saboda yadda aka tsara titin cikin salo na zamani. An gina shi ne a matsayin wani tsari mai ramuka a ciki, wanda zai iya ɗaukar hanyoyin ruwa, wayoyi da bututun ƙarƙashin ƙasa.
Masu ƙirƙirar aikin, Anne Koudstaal da Simon Orritsma, waɗanda ke da alaƙa da kamfanin KWS, sun bayyana cewa an samar da tsarin ne domin rage dogaro da hanyoyin kwalta na gargajiya da ake yawan gyarawa saboda lalacewa.
Aikin farko na gwaji ya fara ne a Zwolle, birnin da hedikwatar kamfanin Wavin ke ciki. An yi amfani da tsarin da aka riga aka ƙera a masana’anta, sannan aka hada shi cikin kwanaki kaɗan a wurin aikin.
Babban abin mamaki a aikin shi ne yadda aka juya sharar roba zuwa wani muhimmin abu na more rayuwa. Robobin da galibi ake zubarwa ko ƙona su sun zama wani ɓangare na gina hanyoyi masu anfani ga jama’a.
Masu aikin sun bayyana cewa babban burinsu shi ne kaiwa ga yin amfani da robobi da aka sake sarrafawa kashi 100 cikin 100 a irin waɗannan ayyuka nan gaba.
Wani abin burgewa kuma shi ne yadda aka tsara cikin titin. Saboda tsarin na da sarari a ciki, ana iya ɓoye bututun ruwa, hanyoyin magudanar ruwa da igiyoyin lantarki a ƙarƙashinsa ba tare da sake fasa hanya ba idan ana buƙatar gyara ko ƙarin aiki.
Kamfanin Wavin ya ce, tsarin yana taimakawa wajen fitar da ruwa cikin gaggawa a lokacin damina, sannan yana rage ƙarar hayaniyar ababen hawa.
Bugu da ƙari, an bayyana cewa wannan sabon tsarin na iya ɗaukar lokaci har sau uku fiye da hanyoyin gargajiya kafin ya lalace, tare da rage yiwuwar samuwar ramuka da tsagewa.
Masana sun ce hakan zai taimaka wajen rage kuɗaɗen gyaran hanyoyi da kuma yawan katse zirga-zirga saboda ayyukan gyare-gyare.
Domin tantance ingancin aikin, an sanya na’urorin lura da yanayi a titin domin bibiyar yanayin zafi, yawan masu amfani da hanyar da kuma yadda titin ke jurewa tsawon lokaci.
Bayan nasarar gwajin farko a Zwolle, masu aikin sun bayyana shirinsu na faɗaɗa aikin zuwa wasu yankuna ciki har da Giethoorn da ke lardin Overijssel domin ci gaba da gwada fasahar.
Masu sharhi kan harkokin muhalli sun bayyana aikin a matsayin wata muhimmiyar hanya ta haɗa kare muhalli da ci gaban more rayuwa, musamman a lokacin da duniya ke fama da matsalar sharar robobi da lalacewar hanyoyi.
