Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta bayyana cewa yankuna 178 da ke cikin ƙananan hukumomi 28 na Jihar Kano na cikin haɗarin fuskantar ambaliya a bana.
Darakta Janar ta NEMA, Hajiya Zubaida Umar, ta bayyana hakan yayin taron wayar da kan masu ruwa da tsaki da kaddamar da shirin shirye-shiryen tunkarar ambaliya na ƙasa na shekarar 2026 a Kano. Ta ce hasashen da hukumar kula da yanayi ta Nijeriya (NiMet) da hukumar kula da harkokin ruwa (NIHSA) suka yi ya nuna cewa wasu yankunan Kano na iya fuskantar ambaliya.
Ta bayyana cewa NEMA ta gano ƙananan hukumomi 28 da ke cikin matsakaicin haɗarin ambaliya, tare da yankuna 178 da ke bukatar daukar matakan kariya na musamman.
Kazalika ta kuma buƙaci mazauna yankunan da ke cikin haɗari su kasance cikin shiri tare da bin umarnin kwashe jama’a idan buƙatar hakan ta taso.
Da ya ke nasa jawabin, Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda kwamishinan albarkatun ruwa, muhalli da sauyin yanayi, Dakta Dahiru ,Muhammad Hashim ya wakilta, ya ce gwamnatin jihar ta amince da matakan rage ambaliya da suka haɗa da share magudanan ruwa, rushe gine-ginen da suka toshe hanyoyin ruwa da kuma shuka bishiyoyi miliyan 10.
Mahalarta taron dai sun jaddada muhimmancin yaɗa bayanan gargaɗin yanayi ga al’umma domin rage asarar rayuka da dukiyoyi sakamakon ambaliya.
