
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sace ‘yar uwar tsohon Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu a Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo.
Iyalan tsohon ministan kuma jigo a jam’iyyar APC ne suka tabbatar da aukuwar lamarin, inda suka ce an yi awon-gaba da Misis Olaide John-Paul da ‘yan biyunta maza masu shekara 12 ne a yau Laraba, 3 ga watan Yuni, 2026.
A cewar sanarwar da ya aike wa manema labarai, mai taimaka wa Adelabu kan harkokin yaɗa labarai, Femi Awogboro, al’amarin ya faru ne da misalinàq ƙarfe 7:30 na safe, yayin da matar ke kan hanyar kai ‘ya’yan nata makaranta.
Misis John-Paul, wadda ita ce ƙaramar ‘ya ga Misis Olufunmilayo Aduke Adegoke Adelabu, ta yi murabus ne daga aiki a First Bank Pension Custodian a shekarar 2025 kana daga bisani ta koma Ibadan tare da ‘ya’yanta.
An ruwaito cewa tana shirin barin Nijeriya ne a halin yanzu domin koma wa Birtaniya ne inda a nan mijinta yake da zama.
Iyalan nata sun bayyana alhinin faruwar al’amarin, amma sun tabbatar da cewa tuni hukumomin tsaro suka fara yunƙurin ceto su tare da kamo dukkan wanda aka samu da hannu a laifin.
Haka kuma, iyalan sun roƙi al’umma da su ƙaurace wa yaɗa labaran da ba a tabbatar da su ba akan al’amarin waɗanda ka iya haifar da tsaiko ga aikin ceton nasu.
