Tinubu ya ƙaddamar da manyan ayyukan CNG a faɗin Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ƙaddamar da manyan ayyukan samar da ababen more rayuwa na iskar gas ta CNG guda huɗu a jihohin Legas, Abuja da Imo, a wani mataki da Gwamnatin Tarayya ta ce zai taimaka wajen rage kuɗin sufuri da kuma bunƙasa amfani da makamashi mai tsafta a ƙasar nan.

Ayyukan, waɗanda aka aiwatar ta hannun Asusun Bunƙasa Ababen More Rayuwa na Iskar Gas (MDGIF), na daga cikin matakan da gwamnatin tarayya ke ɗauka bayan cire tallafin man fetur, domin rage nauyin da ke kan jama’a tare da ƙarfafa amfani da iskar gas a cikin gida.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar, ya bayyana cewa an ƙaddamar da ayyukan ne ta hanyar fasahar sadarwa ta zamani a matsayin wani ɓangare na bukukuwan cika shekara uku da gwamnatin Tinubu ta yi kan mulki.

A yankin Ojota da ke Legas, Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da tashar Portland Gas CNG Mother Station, wadda ke da ƙarfin rarraba iskar gas har mita kubik dubu 96 a kullum. Aikin ya kuma haɗa da manyan motocin jigilar gas guda biyu, wurin adana iskar gas mai ruwa (LCNG) mai nauyin tan 54, da kuma wata tashar CNG da ke Kubwa a Abuja.

Haka kuma shugaban ya ƙaddamar da tashar cika CNG ta kamfanin IBILE Oil and Gas Corporation (IOGC) a Legas, wadda ke jagorantar cibiyar tashoshin CNG guda 15 da ake ginawa a sassan jihar. An tsara tashoshin ne domin samar da makamashi mai sauƙin farashi, rage kuɗin sufuri da kuma rage hayaƙin da motoci ke fitarwa.

A Abuja kuwa, Shugaban ƙasar ya ƙaddamar da babbar tashar ƙarfafa CNG ta kamfanin Rolling Energy Limited tare da haɗin gwiwar MDGIF. An bayyana cibiyar a matsayin ɗaya daga cikin mafi inganci a Yammacin Afirka, inda take da na’urorin matse gas, wuraren ajiya da kuma kayan rarrabawa masu iya yi wa motoci har 1,000 hidima a kowace rana.

Har ila yau, cibiyar na da wurin sauya motocin da ke amfani da fetur zuwa CNG, inda ake iya sauya motoci 20 da babura masu kafa uku 25 a kullum.

A Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Owerri (FUTO), shugaban ƙasar ya ƙaddamar da tashar FEMADEC CNG Daughter Station da Cibiyar Sauya Motoci, ƙarƙashin shirin Tallafin Rage Wahalhalun Sufurin Jami’o’i (SPROUT).

Shirin na daga cikin ƙudurin gwamnati na samar da tsarin CNG a jami’o’i 20 na ƙasar nan, inda zai haɗa da motocin bas masu amfani da CNG, babura masu kafa uku, cibiyoyin sauya motoci da kuma wuraren horas da ma’aikata da ɗalibai.

Gwamnatin Tarayya ta kuma haɗa hannu da cibiyoyin kuɗi ta hanyar Asusun CALM (Credit Access for Light and Mobility) domin samar da rance mai sauƙi ga masu son sauya motocinsu zuwa tsarin amfani da CNG.

Da yake jawabi yayin ƙaddamar da ayyukan, Shugaba Tinubu ya ce makomar makamashin Nijeriya za ta ta’allaƙa ne kan albarkatun iskar gas da ƙasar ke da su, ba wai kan makamashin da ake shigo da shi daga ƙasashen waje ba.

“Nijeriya ƙasa ce mai yalwar iskar gas. Makomar makamashinmu ba za ta dogara da aron wasu ƙasashe ba. Za mu gina ta ne daga abin da Allah Ya hore mana, kuma waɗannan ayyuka da muka ƙaddamar a yau shaida ce ta hakan,” inji shugaban ƙasar.

Ya ƙara da cewa, ayyukan za su taimaka wajen rage kuɗin sufuri, ƙarfafa tsaron makamashi da kuma haɓaka amfani da makamashi mai tsafta a faɗin ƙasar.

Shi ma ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur Mai Kula da Harkokin Gas, Ekperikpe Ekpo, ya ce ayyukan sun nuna ƙudirin Gwamnatin Tarayya na mayar da iskar gas ta cikin gida ginshiƙin sauyin tsarin makamashi da bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya.

A nasa ɓangaren, Babban Daraktan Asusun MDGIF, Oluwole Adama, ya bayyana cewa ayyukan sun nuna irin nasarar da za a iya samu idan gwamnati, hukumomin sa ido, masu zuba jari da ƙwararrun masu fasaha suka haɗa kai wajen aiwatar da manyan ayyukan ci gaba mai ɗorewa.

By ukarofi