Daga JOHN D. WADA a Lafia
Dan takarar jam’iyyar Labour Party (LP) na zaɓen cike gurbin kujerar sanata a jihar Nasarawa Hon. Labaran Maku ya zargi gwamnatin jihar da shirin tafka maguɗi a zaɓen dake tafe.
Maku ya yi wannan zargi ne a yayin taron manema labarai da ya gudanar a garin Akpata kusa da Akwanga a ranar Laraba.
Ya ce akwai kimanin wuraren zaɓe tara da gwamnatin jihar ta yiwa alama a yankin ƙaramar hukumar Nasarawa Eggon inda yawan masu rijista a jerin masu kaɗa ƙuri’a yafi yawa.
Maku ya ƙara da cewa tun da gwamnatin ta san ba za ta iya lashe zaɓen ba kuma tana jin tsoron shahararsa a faɗin yankin, sai ta yanke shawarar cutar da sakamakon zaɓen.
Ya cigaba da bayyana cewa “Idan ka je garuruwan Nasarawa Eggon da Akwanga da Wamba za ka gano cewa Labour Party tana da goyon bayan kashi 80%. Kuma wannan ya samo asali ne daga ayyukanmu na kusa da al’umma da kuma sadaukarwarmu ga hidimomin su a ko yaushe da muke yi. Muna da rahotannin sirrin tarurrukan gwamnati na yadda za su cutar da zaɓen ganin babu wata dama da suke da ita na lashewa,” in ji shi.
Daga cikin abubuwan da Hon. Labaran Maku yake zargin ana shirin yi, akwai amfani da ‘yan daba da aka ɗauka domin rushe tsarin gudanar da zaɓen cikin lumana. Ya kuma roƙi gwamnatin tarayya ta yi wa gwamnonin jihohi musamman na jihar ta Nasarawa gargaɗi kan amfani da jami’an tsaron tarayya wajen haifar da rikici a lokacin zaɓe.
“Gwamnonin jihohi ne ke haifar da rashin tsaro a jihohinsu ta hanyar tilastawa da cutar da sakamakon zaɓe sannan a ƙarshe su zargi shugaba Tinubu. Jama’a za su fito ƙwansu da kwarkwata su kaɗa ƙuri’a amma ƙuri’arsu ba za ta ƙidaya ba kuma wannan na iya haifar da matsanancin rashin tsaro,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa a nasa ɓangaren gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule yana aiki tare da ‘yan sanda domin mayar da shugabannin yankuna da sauran manyan jami’ai kamar yadda suka yi a lokacin zaɓen fidda gwanin APC da ya ƙare cikin rikici.
A cewarsa APC har yanzu ba ta gudanar da zaɓen fidda gwaninta na cike gurbin sanatan ba amma ta tilasta wa al’umma ɗan takara marar karɓuwa inda ya ƙara bayyana cewa yana da kyakkyawan fata cewa jam’iyyar sa ta Labour Party ɗin za ta fito da nasara a ƙarshe.
Maku a ƙarshe ya jaddada cewa al’ummar Nasarawa ta Arewa sun riga sun waye a fannin siyasa kuma ba sa zaɓar ‘yan takara bisa la’akari da jam’iyya illa ƙwarewa da gaskiya kaɗai.
